Yawan masu cutar coronavirus ya ragu sosai a jihar Jigawa sabanin kwanakin baya da aka yi ta samun masu cutar a tsakanin almajirai da ake dawo da su daga wasu jihohi.
Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar ya ce duk da haka jihar za ta ci gaba da zama a kulle har zuwa ranar 15 ga watan Yunin da muke ciki.
Gwamna Badaru ya alakanta raguwar yaduwar cutar da kiyaye matakan da gwamnatin ta sanya na yin amfani da takunkumi da wanke hannu da sauran hanyoyin kare yaduwar cutar.
Badaru ya ce matukar jama’a suka ci gaba da kiyayewa hanyoyin har zuwa wani lokaci za a samu bude jihar domin ci gaba da harkoki yadda aka saba.
Ya kara da cewar an sallami almajirai 1,300 da aka tabbatar ba su kamu da cutar ba yayin da ake ci gaba da killace wasu 23 da suke dauke da ita.
Ya ce shirye-shirye sun yi kan matakan da gwamnatin jihar za ta dauka na bude ofisoshinta a koma aiki matukar babu sauran cutar afadin jihar.