✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba yanzu na fara finafinan barkwanci ba –Aminu Shariff Momoh

Aminu Sharrif wanda aka fi sani da Momoh, jarumi ne, kuma mai shiryawa tare da bayar da umarni a masana’antar fina-finan  Hausa  ta Kannywood. A…

Aminu Sharrif wanda aka fi sani da Momoh, jarumi ne, kuma mai shiryawa tare da bayar da umarni a masana’antar fina-finan  Hausa  ta Kannywood. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana wa masu yi masa kallon ya cana sheakr fitowa a finafinai daga na mugunta zuwa na barkwanci inda ya ce sghi da can da finafinan barkwamnci ya fa shiga masana’antar Kannywood da sauran batutuwa da suka shafi harkar finafinan Haua. Ga yadda hirar da kasance: 

 

Aminiya: An dauki tsawon lokaci ba a ganin kana fitowa a finafinan Hausa ba, me ya kawo hakan? 

Momoh: Ba wani abu ba ne ya sa hakan ba illa komawa gefe da na yi don na yi wa masanaantar kallo na tsanaki domin mu yi kokarin canja akalar masananatar yadda za ta fuskanci wani yanayi da kowa zai amfana da ita. Daga bisani da muka fuskanci gyran ba kadan ba ne don ana bukatar nazari wanda zai kai ga a samar da fasali mai kyau a harkar wanda har na baya za su zo su amfana. har yanzu ana kai, ba a gama ba sai dai muna fatan nan da ba dadewa masana’antar za ta hau kan wani layi don ganin ta yi gogayya da sauran sa’anninta  a fadin kasar nan da duniya gaba daya.

Aminiya: An san ka na fitowa a fannin mugunta, amma sai gashi yanzu ka koma fitowa a finafinan barkwanci mai ya kawo wannan sauyi?

Momoh: To ni dama tun farko da na fara fitowa a fim na fara ne da wasannin barkwanci na zamani wanda muke nuna rayuwar iyali da sauran abin da ya shafi zamantakewar jama’a. Na fara fitowa a wani fim na Kamfanin Dukku koda yake na manta sunansa. Daga nan sai na fito a wani fim nawa mai suna Ayi dai mu gani. A wanann lokaci na yi finafinai kusan guda Biyar kafin na fara fitowa a finafinan 

Aminiya: Ya za ka kwatanta harkar finafinan Hausa yadda take a baya da kuma yanzu, ma’ana an samu wani ci gaba a harkar?

Momoh: Ba za ace ba a sami ci gaba ba, sai dai dan kadan ne, wanda ya shafi yin amfani da damar samun ilimi da masu harkar ke yi da kuma shirya tarurrukan kara wa juna sani da ake yi sai kuma dan kokarin tallafi da hukumomin gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu  ke bayarwa don ganin an bunkasa harkar. Amma a banagren labaru da sauran yadda abubuwa ke gudana za a iya cewa baya ta fi yanzu, domin yawancin labaran da sun fi ma’na da kuma ilimintarwa. Sai dai ’yan kadan ne a yanzu ke yin kokarin ganin sun sami labarai da suka shafi ci gaban mutane ba wai kawai nishadi ba.Yawanci dama an fi sanya wakokin ne a finafinan soyayya.

Lokaci ya yi da masu shirya fim ma za su canza akalar jigon labarunsu daga na soyayya zuwa wasu al’amura da suka shafi rayuwar al’umma kamar batun yawan mutuwar aure da auren wuri da danne hakiin dan adam da dogaro da kai don bunkasa tattalin arziki da kuma kokarin ciyar da harkar ilimi gaba a yankin Arewa da sauransu.

Aminiya: An dade ana batun kawo gyara game da tsarin tufafin ’yan matan da ke fitowa a finafinai da kuma batun rawa da waka, ya za a yi a magance wannan matsala?

Momoh: To anan za mu iya cewa zamani ne ya kawo hakan, idan kin duba al’umarmu za ki ga irin wadannan sutura da ake magana akai suma da su suke amfani. Kasancewar su ’yan fim suna kwaikwayon rayuwar al’ummar da suke ciki ne ya sa suke amfani da irin wadannan sutura. Sai dai bai kamata a zurfafa amfani da wadannan suturu ba don kada mai kallo ya yi tunanin ana goyon bayan yin amfani da wadannan sutura ne. Sai dai ina kira domin a kawo gyara a harkar, ma’ana a yi amfani da sutura da suka kamata.

Batun rawa da waka kuwa an dade ana muhawara akai, mun yi ittifakin cewa ba abu ne da yake nuna zahirin rayuwar Bahaushe ba, domin ko a can Indiyan da ake kwaikwayon su a wannan fanni rayuwarsu ta zahiri ba haka take ba. Ana sa wakar ne kawai don nishadi. Ni ina ganin ba sai an yi rawa da waka a fim sannan zai karbu a wajen ‘yan kallo ba, idan labari ya tsaru shike nan. Ni abin da na fi yi shi ne ina sanya wakar ne a karkashin hoto.  

Aminiya: Mece ce matsalar kasuwancin finafinai a halin yanzu? 

Momoh: Babbar matsalar kasuwancin fim ita ce masu satar fasaha. Misali masu downloading fim suna turawa a wayoyin hannu babu shakka wadanan mutane suna kassara harkar kasuwancin fim. Hakan ya sa aka zauna da su don ganin an gano bakin zaren. A yanzu dai an nemi su yi rajista tare da neman su bayar da ‘yan wasu kudi da za a rika karbar fim bayan ya fita daga bangaren sinima da bangaren da ake bugawa, idan mutum ya yi rajista za a ba shi kwafe wanda za a sa wata kebentacciyar lamba a jiki. Idan kuma aka samu mutum yana tura fim ba shi da wannan lamba za a dauki matakin shari’a akansa. Muna sa rai nan ba da dadewa ba za a fara amfani da wannan tsari.

Aminiya: Wane albishir kake da shi ga masoyanka?

Momoh: Albishir din da nake da shi gare su shi ne muna nan muna kokari wajen ganin mun tsaya kan abin da muke yi na fadakar da mutane, don ganin mutane sun dauki darasi game da hakan yada za a samu gyara a harkar zamantakewar al’ummarmu. A matsayinmu na ‘yan Adam masu kuskure, ya kamata masu kallonmu su rika yi mana uzuri idan an ga wani abu ba a yi daidai da a ddini ko al’ada ba. Idan ana da wasu shawarwari ko korafi akwai hanyoyin da za a tuntubi wanda abin ya shafa don zama a tattauna yadda za a gyara kurakuran kai tsaye amma ba a zauna ana Allah wadai da mutum ba. Muna bukatar shawarwari daga malamai da shugabanni da kowane rukuni na al’umma don ganin an tunkari wasu matsaloli da ke tasowa a cikin al’ummarmu don gudu tare a kuma tsira tare.

Aminiya: ka yi batun a rika ba ‘yan fim shawarwari don gyara, to me ye sa a lokuta da dama idan malamai sun ja hankalinku game da wasu kurakurai musamman wadanda suka shafi addini sai ‘yan fim ku yi ca akansu?  

Momoh: Ba haka ba ne, ba wai gyaran ne ba mu so ba, abin da yake faruwa shi ne son zuciya da suke nuna wa a gyaran ko shawarwarin na su ne yake janyo wa a yi musu ca. Akwai manyan malamai da suke za ma da mu su nuna mana kurakuranmu ta hanyar kafa mana hujja da ayoyn Al’kurani da Hadisai. Haka kuma akwai malaman da suna yi maka magana ka san ra’ayinsu ne ba wai gayar za su yi ba, wanda kuma hakan ba komai yake nuna wa sai kiyayaya da hassada. Kin san idan aka samu cewa kai kana fadakarwa wani ma yana fadakarwa kowa akwai hanyarsa da kuma mabiyansa daban, to dole akwia wannan kishin ko gasa a tsakani. Abin da muka dauka shi ne duk malamin da zai zo a gaskiya bisa doron gakiya za ka ga cewar wanann mutumi yana tafiya kafada-kafada da mu da marubuta a ko ina a duniya. Amma duk wanda zai dauko ra’ayinsa ya shiga rigar addini ya fake za ki ga mun yi tir da shi kuma su ma al’umma sun yi tir da shi, domin mun san ba wani sani ne yake da shi ba. 

Yanzu misali idan kika dauki batun kauyen yin finafinai da aka yi yunkurin kafa shi a Kano, haka malaman nan suka fito suka yi tir da lamarin, a maimakon su zauna su samo wasu hanyoyi na gyara da za a yi a harkar. Wasu daga cikinsu ma ba su fahimci abin ba, an gaya musu ne abaibai ne, domin magana ta gaskiya abin nan abu ne da muka yi asara, domin zai haifar mana da ci gaba sosai a harkar da ma jihar gaba daya. Yanzu ga shi nan muna ji muna gani Jihar Kaduna ta samu abin. Ya kamata dai a duk lokacin da aka kawo wani sabon abu mutum ya tsaya ya fahimce shi kafin ya fito ya fara sukarsa.