Barkanmu da warhaka Manyan gobe yaya hutu? Da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin “Ba wawa shawara bata lokaci ne”. Labarin ya kunshi yadda bai wa mara hankali shawara ya zama tamkar bata lokaci. A sha karatu lafiya.
Akwai wasu tsuntsaye a wani daji, A kowane lokaci kafin isowar damuna za su kintsa sosai. Haka suka yi a wannan damuna, kowane tsuntsu ya fita ya nemo itatuwa da fuka-fuki domin sanya wa a gidajensu ta yadda iska ko ruwa ba za su yi musu illa ba.
Bayan sun gama gyaran gidajen nasu, sai suka fita neman abinci wanda zai ishesu har zuwa karshen damina.
Ana cikin haka, sai damuna ta iso. kowanne daga cikinsu suka samu mafaka ban da wani biri da ya hau kan bishiyar da wadannan tsuntsayen suka yi gidajensu.
Biri ya na kakkarwa da jin sanyi, ga shi ya jike sharaf! Saboda tausayi sai wani tsuntsu ya ce da birin da ka shiryawa wannan damunan da hakan bai faru da kai ba. Sai wata tsuntuwa mai ’ya’ya ta ce, ga shi gidanmu ba shi da girma da mun taimaka maka. Wannan kalami da tsuntsuwar ta yi sai ya bata wa birin rai inda ta kai sai da ya rusa mata gidan da ta fake da ’ya’yanta.
Daga nan sai sauran tsuntsayen suka yi nadamar abin da ya sa suka bai wa birin shawarar da ta harzuka shi har ya dauki mataki a kan daya daga cikinsu.
Daga nan suka gane cewa bai wa wawa sharawa tamkar bata lokaci ne.