✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba wanda ya isa ya tilasta min karbar rigakafin Coronavirus —Djokovic

Duk abin da ya shafi lafiyar jikina ya fi min duk wata lambar yabo ko kudi da zan samu.

Fitaccen dan wasan Tennis, Novak Djokovic ya ce ya gwammaci a yi babu shi a duk wata gasar Tennis da za a yi nan gaba da a tilasta masa karbar rigakafin Coronavirus.

Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito Djokovic a wata ganawa da manema labarai yana cewa kada a danganta shi da kungiyar masu adawa da rigakafi, amma kuma ya goyi bayan a bai wa kowane mutum dama ta yin zabin karbar rigakafin ko sabanin haka.

Da aka tambayi Djokovic ko zai iya hakura da shiga gasa kamar su Wimbledon da French Open saboda ra’ayinsa a kan rigakafi, sai ya kada baki ya ce, “kwarai, abubuwa ne da na yi niyyar sadaukarwa.”

A watan da ya gabata ne hukumomin Australia suka tisa keyar dan wasan da ya lashe manyan kofunan Grand Slam sau 20 gida, sakamakon sa-in-sa a game da tirjewarsa a kan rigakafi, duk da cewa ya karbi izinin likita na shiga kasar bayan da ya murmure daga cutar COVID-19 da ta kama shi.

Dan wasan wanda shine lamba daya a wasan Tennis ya ce ya kafe a kan haka ne saboda yanke shawara a kan abin da ya shafi jikinsa ya fi masa duk wata lambar yabo ko kudi da zai samu.