✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ni da tabbas ko Ederson zai ci gaba da zama a Etihad — Guardiola

Ana ci gaba alaƙanta Ederson da komawa taka leda a Saudiyya.

Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya ce ba shi da tabbas ko Ederson zai ci gaba da zama a ƙungiyar kakar wasa ta bana.

Furucin Guardiola na zuwa ne yayin da ake ci gaba da alaƙanta mai tsaron ragar tawagar Brazil da cewar zai koma tamaula a babbar gasar tamaula ta Saudiyya.

Guardiola ya sanar a karshen kakar da ta wuce da cewar Ederson ne zai ci gaba da tsare ragar City, amma kuma sai ya yi amfani da Stefan Ortega a wasan farko zagayen kwata fainal da Real Madrid a Gasar Zakarun Turai.

A lokacin da ya gana da manema labarai bayan da Celtic ta doke City 4-3 a wasan sada zumunta a Amurka, Guardiola ya ce “zan so ya ci gaba da zama a Etihad, amma hakan ya alaƙanta daga wasu ƙungiyoyin.”

Ederson ya shiga wasan da Celtic ta doke City a Chapel Hill a zagaye na biyu, shi ne wasan farko da mai riƙe da Firimiyar Ingila ta yi na shirin tunkarar kakar bana.