Gwamnan Jihar Abiya, Okezie Ikpeazu, ya musanta rade-radin da ke yawo cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar PDP.
Gwamnan ya musanta zargin ne a cikin wani shiri na musamman da ya yi da gidan rediyon jihar a ranar Asabar.
- Gwamnan Abia ya ba ‘yan kwangilar Gwamnatin Tarayya wa’adi
- Coronavirus: An killace Gwamnan Abia Ikpeazu
A cewar gwamnan, bai ga dalilin da zai sanya shi barin jam’iyyar PDP ba a halin yanzu.
Ya kara da cewa a wasu jihohin, da zarar gangar siyasa na kadawa sai ka ga ’yan siyasa sun shiga wasan sauya sheka.
Sai dai ya ce PDP a jihar Abiya, ta samar da dukkanin abin da mutanen jihar ke bukata, don haka batun sauya sheka bai ma taso ba.
Ya kuma ce har yanzu a Jihar l babu wanda ya gamsar da shi cewa akwai wata jam’iyya da ta fi PDP.
Ya ce a matsayinsa na shugaban gwamnonin PDP a Najeriya, ya gwammace ya zama ‘yaron mota da ya zama direba mara amfani’.