Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya sanar da cewa ba ya da sha’awar zama Shugaban Kasar Najeriya.
Sarki Sanusi wanda kuma shi ne Halifan Darikar Tijjaniyya na Najeriya, ya bayyana hakan ne yayin wani taron gabatar da makaloli na shekara-shekara da aka gudanar kan cikarsa shekara 60 a duniya a ranar Asabar.
A cewarsa, abin da zai mayar da hankali a kai a yanzu shi ne zama malamin jamia bayan ya kammala digirin digirgir a wata jami’ar birnin Landan.
Ya ce kasancewar ba shi da ra’ayin shiga siyasa a halin yanzu, ba kuma zai kutsa kansa cikin lamarin da ba shi da ido a cikinsa ba.
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya ce, “Ban boye burina ba na son zama Sarkin Kano, haka kuma ban taba boye wani buri ba a rayuwata na duk abin da nake da shaawarsa.
“Saboda haka idan na ce ba ni da sha’awar shiga siyasa, ba ni da ra’ayinta ne ko kadan kuma ban dauko hanyarta ba ko a baya.
“Idan ina son shiga harkar siyasa, zan fito karara na bayyana cewa zan yi takarar Shugaban Kasa.
“Ni dan Najeriya amma bani da ra’ayin shiga siyasa saboda ban gina kai na a kan hakan ba.
“Tun fil azal na dauko hanya tare da tsara rayuwata a kan harkar ilimi da karantarwa, na shirya wa zama Sarki sannan na shirya shiga aikin banki.
“Amma ko sau daya ban taba tunanin shiga harkar siyasa ba, don bai kamata mutum ya jefa kansa cikin lamarin da ba shi da ido a cikinsa ba dole sai an zauna an koya.”
A cewar tsohon Sarkin, zai koma kan tsarin koyo da karantarwa domin ita ce hanyar da ya dauko tun asali.
“Na fara gina rayuwa ta a kan tsarin koyo da karantarwa a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sannan daga baya na watsar na koma harkar aikin banki.
“Na shiga harkar aikin banki, sannan kuma na zama Sarki. Saboda haka a yanzu ina son karasa wancan burin na rayuwa ta da na dauko kuma na watsar a baya.
“A yanzu haka na samu gurbin karatu a jami’ar Landan, inda zan yi digirin digirgir a fannin nazarin Shari’a da Doka.”