✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ni da matsala da Shugaba Buhari – Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya bayyana cewa ba ya da wata matsala ta kashin kai a tsakaninsa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari…

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya bayyana cewa ba ya da wata matsala ta kashin kai a tsakaninsa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ko tsakaninsa da wani mutum illa dai shi a kullum yana magana ne kan al’amuran da za su kawo kyautata rayuwa a tsakanin ’yan Najeriya.

Saraki ya yi wadannan Kalamai ne a Bauchi lokacin da yake neman alfarmar masu zaben fid-da-gwani na dan takarar Shugaban kasa daga Jihar Bauchi, ya ce a kullum yana maganganu ne a kan al’amuran da ke damun ’yan Najeriya don ganin an samu mafita, “Kuma babban damuwata ’yan Najeriya sun shiga cikin mawuyacin hali na kuncin rayuwa sakamakon jefa jama’a cikin yunwa da fatara da gwamnatin APC ta yi, wanda hakan ya samo asali ne bisa rashin cika alkawuran da muka dauka lokacin yakin neman zabe don kawo sauyin da zai kyautata rayuwar al’ummar Najeriya.”

Ya ce “Matasanmu suna fama da rashin aikin yi, sha’anin ilimi ya tabarbare. Babu hanyoyin samar da sana’a, wanda hakan na barazana ga tattalin arzikin kasar nan. Wannan tsananin yanayin da ake ciki na talauci da fatara da jama’ar kasar nan suke fuskanta da matsalolin tsaro da wuyar samun mai duk sun addabi kasar nan, yau Najeriya tana fama da matsalar rashin ilimi kuma matsalolin ta’addanci duk sun kewaye Najeriya.”

Saraki ya ce, “Najeriya tana fuskantar matsalar fadace-fadace da rikicin manoma da makiyaya, da saura matsalolin da suke jibge a Najeriya an kuma gaza samar da tsare-tsaren da za su kawo mafita don kyautata rayuwar gobe. Saboda haka na daura niyyar cewa zan ci gaba da kokari don samun Shugabancin kasar nan da nufin fitar da Najeriya daga wadannan matsaloli,” inji shi.

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Bauchi, Hamza Akuyam ya ce da yardar Allah PDP za ta kwace mulki a hannun APC a zaben 2019 domin ci gaba da yi wa jama’ar kasar nan hidima.

Akuyam ya gode wa Saraki bisa bai wa jam’iyyar reshen Jihar Bauchi gudunmawr Naira miliyan 20 lokacin zaben cike-gurbi na Sanatan Bauchi ta Kudu, ya kuma gode wa Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara bisa dawowa cikin Jam’iyyar PDP da ya yi,

Tsohon Ministan Abuja Sanata Bala Mohammed ya bayyana kyakkywan Jagoranci da hakurin Saraki wanda ya ce mutum ne da ya gaji mahaifnsa kuma a kullum damuwar Najeriya da ci gaban kasa ne ya sa a gaba. Ya yi alkawarin cewa masu zaben fid-da-gwani daga jihar ba za su ba shi kunya ba.