✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba na zargin matan fim — Naziru Dan Hajiya

Ai ba zai yiwu ba a ce ni ne zan fadi abubuwa marasa kyau game da abokan sana’ata.

Naziru Auwal wanda aka fi sani da Naziru Dan Hajiya fitaccen forodusa ne a Masana’antar Kannywood, ya daɗe ana damawa da shi a masana’antar.

A kwanakin baya an yi ta yada wata magana cewa ya ce bai san inda jaruman Kannywood mata ke samun kudi ba.

A tattaunawarsa da Aminiya, ya fayyace abin da ya fada da abin da yake nufi da makomar Kannywood a gaba:

A kwanakin baya an yi ta yada wata magana cewa ka ce ba ka san inda matan Kannywood suke samun kudi ba, me kake nufi da wannan magana?

Ba haka nake nufi ba. An juya min magana ce kawai. Me ya sa ma zan fadi haka? Wadannan jaruman mun san su, na san harkokin da suke yi na kasuwanci.

Na san shagunansu, inda suke sayar da takalma da riguna da sauran kasuwancinsu. Sannan bayan kasuwancinsu, wasu na ci gaba da taka rawa a fim din nan.

Ai ba zai yiwu ba a ce ni ne zan fadi abubuwa marasa kyau game da abokan sana’ata. An juya min magana ce.

Kuma kafin ka ce kwabo ta zagaya sosai, shi ya sa na yi shiru ina kallo. Amma har ga Allah ban fada ba, ba zan taba cin mutuncin abokan sana’ata ba.

Yaya jarumai mata abokan sana’arka suka dauki maganar, sun caccake ka?

Abin mamaki kuma ko da suka ji maganar da ake ta yadawa ba su soke ni ba. Wannan saboda muna da fahimta mai kyau da su ne.

Gaskiya muna zama lafiya da su. Ina tunanin bai wuce biyu daga cikinsu ba da suka yi magana.

Suma dariya kawai suka yi suka ce sun san cewa ba halina ba ne, su ma suna mamaki. Sannan sun san cewa ba zan yi wani abu da zan cutar da su ba.

Kawai sai na kara musu bayani cewa an juya min magana ce, amma ga abin da nake nufi. Shi ke nan kuma maganar ta wuce. Ba a ta yamadidi da maganar ba kamar yadda aka yi zato.

Wasu na ganin ai abin da ake zato ne yanzu ya fito daga bakin daya daga cikin manyan forodusoshi na masana’antar, me za ka ce?

Kawai masu yadawa sun yi ne domin neman suna a kafofin sadarwa. Kawai neman magana suka yi.

Idan har zan ga abu mara kyau a tare da abokan sana’ata, idan ba zan iya yi musu magana su gyara ba, ai gara in yi shiru.

Ina kara fada wa mutane cewa wadannan jaruman fa abokan sana’ata ne, ba zan yi wani abu sa zai bata musu suna ba.

Mu koma Masana’antar Kannywood, yaya kake kallon masana’antar a bana?

Mun shigo wannan shekarar da kafar dama. Manhajojin Netflix da Amazon Prime duk sun shirya haska finafinan Kannywood, wanda ba hakan nasara ce babba a gare mu.

Yanzu finafinanmu za su inganta, su bunkasa. Dole za mu kara kaimi wajen shirya finafinai masu inganci.

Tuni mun fara nemo hanyoyin karbar basussuka daga irin su Bankin Masana’antu wato Bank of Industry da sauransu.

Sannan wani karin armashi shi ne naɗa ɗaya daga cikinmu a matsayin Shugaban Hukumar Fim ta Nijeriya wato Ali Nuhu.

Ka ga shi mutum ne wanda ya san matsalolinmu. Ba Kannywood kadai ba, har Nollywood ya santa, ya san matsalolinta.

Don haka an naɗa wanda ya dace, wanda muke da yakinin zai inganta harkar fim baki daya a Nijeriya baki daya, ba Kannywood kadai ba.

Mafi karanci za a samu karin haɗin kai a tsakanin Kannywood ta Arewa sa Nollywood ta Kudu. A takaice dai mun shigo wannan shekara da kafar dama a masana’antar fim.

Za a iya cewa fara sanya finafinan Kannywood a Netflix da Amazon zai magance matsalolin Kannywood?

Idan dai za mu ci gaba da yin finafinai masu kyau da inganci, manhajojin nan za su riƙa karba suna haskawa kuma mu samu manyan kudade.

Don haka, idan za mu rika yin abin da ya dace, zan iya cewa kashi 70 zuwa 80 na matsalolinmu sun kau.

Babbar matsalarmu dama ta kasuwanci ne. Muna da labarai masu kyau, yanzu gyara za mu yi a bangaren shiryawa da daukar finafinan.

Ina tabbatar maka cewa muna yin abin da ya dace, to nan da dan lokaci kalilan za mu ba duniya namaki.

Wane fim kake aiki a kai yanzu?

Fim din Zullumi ne nake aiki a kai yanzu. Ni ne na shirya shi. Fim ne a kan rayuwar jami’a da karatu da rayuwar dalibai baki daya.

Fim ne mai inganci sosai da in sha Allah zai kayatar da masu kallo. Ina musu bushara da wannan fim din, su saurare mu.

Yanzu da kasuwar fim din ta bude, wane kira kake da shi zuwa ga forodusoshin Kannywood?

Kowa ya shirya, ya fara shirya finafinai masu kyau da inganci. Idan ba ka da jari, ka nemi wani ku hada hannu Ku yi aiki mai kyau.

Sannan akwai bankuna da suke ba da bashi. Kawai tsarinka za ka mai musu a rubuce, su duba, idan ya yi za su ba ka kudi.

Idan har ka shirya fim mai kyau, manhajojin na a shirye suke su karba kuma za su ba ka kudade masu kyau da za ka biya bashinka, ka samu riba.

Ka yi maganar hadaka, kana ganin za a iya samun hadaka a Kannywood kuwa kasancewar dama tana fama da rashin hadin kai?

Ai yanzu haɗin kai ya zama dole. Idan a da za ka iya shirya fim da misali Naira miliyan uku zuwa 10, yanzu ana maganar Naira miliyan 20 zuwa 100 ne.

Ka ga idan kana da kudi za ka iya hakada da wani ku tashi kudi mai nauyi a shirya fim babba