✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba na takun saka da kowa – Sambo Dasuki

Bayan da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta sako tsohon mai ba da shawara kan tsaro na kasar, Kanal Sambo Dasuki. Ya dai shefe…

Bayan da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta sako tsohon mai ba da shawara kan tsaro na kasar, Kanal Sambo Dasuki.

Ya dai shefe shekara hudu a tsare, kuma ya ce har yanzu ina ciki koshin lafiya babu abin da ke damunsa kuma ya ce ya samu iyalansa cikin koshin lafiya. Ya kuma gode wa Allah.

A yayin tattaunawarsa da Muryar Amurka VOA Hausa, ya ce bai da wani kira ga gwamnati tarayya, “Ba wani abu da zai faru face abin da Allah Ya tsara, rashin tawakkali shi kesa mutum ya shiga cikin wani yanayi, ba a abin da zance ga gwamnati na yi shekaru hudu a tsare kuma ina lafiya, abin da Allah ya tsara kenan kullum abin da liman yake fada kenan a masallaci ku yi adalci ku rike gaskiya, akwai dalilin da yasa liman ke fadin hakan kenan a saurare shi a hudubar sallar Juma’a.

Ko lokacin da nake tsare ina zuwa kotu kuma na ce, duk lokacin da aka sake ni zamu ci gaba da shari’a, daman a shirye nake.

“Na fi karfin nayi takun saka da kowa.”