✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba na rigima da duk abokin sana’ata- Ali Nuhu

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Ali Nuhu ya bayyana cewa baya rigima ko batanci ga duk wani abokin sana’arsa. Ali Nuhu ya wallafa hakan ne a…

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Ali Nuhu ya bayyana cewa baya rigima ko batanci ga duk wani abokin sana’arsa.

Ali Nuhu ya wallafa hakan ne a shafinsa na kafar sadarwa ta facebook, inda ya umarci masoyansa da su daina cin mutuncin kowa.

“Ina rokon duk masoya maza da mata ku daina yin rubutu a kafar sadarwa dominn cin mutunci  wani ko wata. Ba na rigima ko batanci ga duk wani abokin sana’ata sannan duk wanda ya yi min ku bar shi da Allah. Babu sakayyar da ta wuce ta Allah.”