✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba na bukatar shawarar Ronaldo – Bale

dan wasan kasar Wales da ke buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Gareth Bale ya ce ba ya bukatar shawara daga Cristiano…

dan wasan kasar Wales da ke buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Gareth Bale ya ce ba ya bukatar shawara daga Cristiano Ronaldo dan kasar Portugal game da bugun tazara.
Bale ya jefa kwallaye biyu a bugun tazara a gasar cin Kofin Nahiyar Turai a wasa biyu, shi kuma Ronaldo ya gaza jefa ko kwallon daya duk da cewa ya gwada bugun tazara har sau biyar a yayin gasar da ke gudana a kasar Faransa.
 Bale ya ce, “Ina da nawa tsarin, sannan Ronaldo yana da nasa tsarin duk da cewa muna yin gwaji tare a wurin atisaye amma dai ina son nawa tsarin.”