Hedikwatar Jam’iyyar APC ta Kasa ta karyata labarin da ke yawo cewa ta zabi Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, a matsayin dan takarar shugaban kasar jam’iyyar.
Kwamitin Gudanarwa na Kasa na Jam’iyyar APC na Kasa (NWC) ne ya sanar da haka a yammacin ranar Litinin.
- Dole dan Kudu ya yi takarar shugaban kasa a APC —Gwamnonin Arewa ga Buhari
- Tinubu ya bai wa mutanen da aka kai wa hari a coci tallafin N75m
Jam’iyyar ta sanar da hakan ne bayan bullar wani labari da ke cewa ta zabi Ahmad Lawan a matsayin dan takara tilo, a yayin da ake shirin gudanar da zaben dan takarar shugaban jam’iyyar a ranar Talata.
Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Sulaiman Argungu ya ce labarin kanzon kurege ne ake yadawa game da daukar Ahmad Lawan.
Ya bayyana cewa gwamnonin jam’iyyar daga yankin Arewa da kuma Kudu sun yi ittifaki cewa a bai wa dan yankin Kudu takarar, don haka babu yadda za a yi sabanin hakan.
Aminiya ta gano cewa jam’iyyar ta tashi haikan wajen ganin ta fitar da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023 ta hanyar masalaha, babu hamayya.