✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu yi wa alhazai rangwame wajen canjin Dala ba – CBN

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce ba gaskiya ba ne batun da ake cewa zai samar wa mahajjata Dalar Amurka a farashi mai rangwame a…

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce ba gaskiya ba ne batun da ake cewa zai samar wa mahajjata Dalar Amurka a farashi mai rangwame a yanzu ba.
A makon jiya ne wasu kafofin yada labarai suka ruwaito cewa CBN zai samar wa mahajjata Dala bisa farashin Naira 197 a kan kowace guda, sabanin yadda ake siyarwa a yanzu wato a kan kimanin Naira 310.
A wata sanawar da CBN ya fitar ranar Talata, Gwamnan  Bankin Godwin Emefiele ya ce bankin da hukumar alhazai sun cimma matsaya ne tun lokacin da yake sayar da Dala a kan Naira 197, amma ba yanzu da ta haura 300 ba. Ya ce kuma a kan hakan ne za a bai wa alhazan.
Ya ce an bi duk tanade-tanaden da suka kamata kamar yadda aka saba a kowace shekara.
“Abin da ake yi a kowace shekara shi ne, gabanin fara jigilar alhazai, hukumomin alhazai na Musulmi da na Kirista suna tuntubarmu don cimma matsaya a kan yadda za a samar wa masu ziyarar ibada Dalar Amurka wato maganar kudin guzuri ke nan. Kuma a bana an kayyade kudin ne tsakanin Dala 750 zuwa dubu daya,” inji shi.
Daga nan, ya ci gaba da cewa maganar samar musu da Dala daya a kan Naira 197, magana ce da aka yi ta tun a watan Afrilun da ya gabata, bisa la’akari da yanayin farashin Dala a lokacin, kamar yadda ya bayyana. Ya ce kuma hakan ya shafi duka maniyyata ne wato Musulmi da kuma Kiristoci masu ziyara birnin Jerusalem a bana.
Har ila yau, Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ya ce batun farashin Dala da ake yi, batu ne da hukumar da kuma CBN suka cimma matsaya tun a watan Maris da ya gabata, lokacin yana sayar da ita a kan Naira 197.