✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba mu muka ce CBN ya bijire wa umarnin Kotun Koli kan canjin kudi ba – Fadar Shugaban Kasa

Fadar ta ce ba da yawunta aka ki bin umarnin ba

Fadar Shugaban Kasa a ranar Litinin ta ce sam ba ta umarci Babban Bankin Najeriya (CBN) da Ministan Shari’a, Abubakar Malami su ki bin umarnin Kotun Koli kan ci gaba da amfani tsofaffin kudi ba.

Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

A makon da ya gabata ne dai Kotun Kolin Najeriya ta yanke hukuncin ci gaba da amfani tsofaffin takardun N1,000 da N500 da kuma N200 har zuwa ranar 31 ga watan Disamba mai zuwa.

Garba Shehu ya ce ba Buhari ne ya umarci Gwamnan CBN, Godwin Emefiele da Ministan Shari’a, Abubakar Malami, su ki bin hukuncin ba, inda ya ce hasali ma ba sa bukatar umarninsa kafin aiwatar da shi.

Game da batun zargin da ake yi cewa Shugaban ba shi da tausayi, Fadar ta ce a tarihin Najeriya, ba a taba gwamnatin da ta fito da manufofin da suka taba rayuwar masu karamin karfi kai tsaye kamar ta Buhari ba.

Sanarwar ta kuma ce gwamnatin ba ta taba yin wani abu ko tana sane ko kuma da ganganci ba domin ta bijire wa umarnin kotu, musamman a kan batun canjin kudin.

“Shugaban Kasa ba dan kama-karya ba ne, saboda haka, ba zai taba yin kowanne irin abu don hana Gwamnan na CBN da Ministan Shari’a aiwatar da kowanne irin umarnin kotu ba.

“Umarnin Shugaban Kasa bayan taron Majalisar Magabata ta Kasa shi ne dole bankuna su samar da wadatattun kudaden da ake bukata a kasa su rika yawo, kuma wannan matsayin sam bai canza ba har yanzu.

“Sanin kowa ne Buhari mutum ne da ke mutunta bangaren shari’a da kuma kotuna, kuma a cikin shekarunsa takwas bai yi wani abu da zai kawo cikas ga tsarin ba ko kuma ya yi masa kafar angulu, saboda haka babu dalilin da zai fara yin haka yanzu da yake shirin mika mulki,” in ji Fadar ta Shugaban Kasa.