✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu ji dadin rashin ta’aziyyar gwamnati kan kisan Sheikh Albani ba – Sheikh Lau

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya nuna rashin jin dadi kan yadda har yanzu Gwamnatin Tarayya…

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya nuna rashin jin dadi kan yadda har yanzu Gwamnatin Tarayya ta kasa fitowa ta yi wa al’ummar Musulmin Najeriya jaje da ta’aziyya game da kisan gillar da ’yan bindiga suka yi wa Sheikh Muhammad Auwal Albani a makon jiya a Zariya ba.
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce “yana da kyau Gwamnatin Tarayya ta fito ta yi mana jaje kan wannan al’amari, amma har yanzu ba ta yi mana ta’aziya kan wannan kisan gilla da aka yi wa Sheikh Albani ba. Duk da cewa marigayi Sheikh Albani ya kai matsayin a yi wa al’ummar Musulmin Najeriya jaje da ta’aziyar rashinsa.”
Shugaban ya ce hakkin gwamnati ne ta tsare rayukan al’umma da dukiyoyinsu da mutuncinsu da addininsu. “Don haka muna sauraron mu ji mene ne sanadin wannan kisan gilla da aka yi wa wannan bawan Allah daga wurin gwamnati.”
Ya ce kungiyar Izala tana cike da bakin ciki kan wannan kisan gilla da aka yi wa Sheikh Albani, kuma wannan kisan gilla ya kara wa kungiyar kaimi kan ci gaba da da’awa.
Sheikh Bala Lau ya karshen marigayi Sheikh Albani ta yi kyau, domin duk mai da’awa yana son karshensa ya kasance a cikin da’awar. Saboda Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda ya rasa ransa a cikin da’awa ya yi shahada. “Abin bakin ciki kawai shi ne an rasa Sheikh Albani a lokacin da ake da bukatarsa,” inji shi.
Ya yi kira ga al’ummar Musulmi su ci gaba da yin addu’o’i a masallatai da makarantu da nufin Allah Ya tsare su kuma Ya tona wa masu irin wannan hali da masu daure musu gindi asiri.