✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu janye batun korar Rahama Sadau ba – MOPPAN

Qungiyar masu shirya fina-finan Hausa, Motion Pictures Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN) reshen Jihar Kano, ta karyata batun jita-jitar da ake yadawa cewa ta janye…

Qungiyar masu shirya fina-finan Hausa, Motion Pictures Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN) reshen Jihar Kano, ta karyata batun jita-jitar da ake yadawa cewa ta janye batun korar da ta yi wa fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Rahama Sadau.

Kungiyar ta bayyana hakan ne ta bakin Sakatarenta Salisu Mohammed Ofisa a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a ranar Lahadi.

Ya ce, “To, abin da ya faru a gurguje shi ne, Rahama Sadau ta shigo Kano, ta samu Ali Nuhu kamar suna da wata matsala tsakaninsu, sun sasanta kansu, kuma daga nan ta yanke shawarar za ta nemi afuwar shugannin masana’antar fim, inda Ali Nuhu ya kai ta Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, wurin Afakallahu, sannan ta kawo mana wasika a nan MOPPAN, inda ta ba shugaban kungiyar, Kabiru Maikaba, tana neman a yi mata afuwa, a dawo da ita masana’antar fim ta ci gaba da aikinta.

Ya ce har zuwa yanzu babu wani hukuncin da kungiyarsu ta dauka tun lokacin da ta kai musu wasikar, “Mu a kungiyar MOPPAN ba mu zauna mun daddale don mu kalli takardarta ba, saboda ba MOPPAN kadai ta kore ta ba, akwai wadansu kungiyoyin ’yan fim da suke karkashinta, sai an kira shugabancin kowace kungiya, kamar yadda aka zauna da su kafin aka sallame ta.”

Ya ce, a yayin zaman za su duba bayaninta, tun lokacin da aka kore ta yau shekara guda ke nan, “me ya biyo baya? Wadanne irin kalamai ta yi? Ta ci gaba da aikata ire-ire laifukan da suka sa aka kore ta? Shin akwai nadama a tattare da ta? Sai mun tattauna wadannan batutuwa kafin mu ga irin shawarar da za a dauka, don a yafe mata a dawo da ita, ko kuma a dage mata wannan korar ta zama ta wucin gadi zuwa wani lokaci, ko a ci tararta, ko ma a ki yarda ta dawo.”

Ya bayyana dalilin da ya sa ba su yi zaman ba shi ne, shugaban da zai jagoranci zaman, wato Kabiru Maikaba ba shi da lafiya, an yi masa aiki a idonsa, “kuma babu shakka halartarsa zaman yana da matukar muhimmanci, shi ya sa muka ga bai ma dace a yi zaman ba ya nan ba, idan ya samu sauki, to mako na gaba mu yi zaman.”