Tawagar masu sanya ido da ke wakiltar kungiyar Turai ta EU a zaben shekarar 2015 sun yi watsi da jita-jitar da ke yawo cewa sun goyi bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayin da suke aikin sanya ido a zaben kasar.
Shugaban tawagar masu sanya idon, Santiago Fisas ne ya bayyana haka yayin da yake amsa tamabayoyi daga manema labarai a Abuja.
Fisas wanda har ila yau memba ne a majalisar turai ya ce aikinsu ya mayar da hankali ne kan yadda za su inganta damokradiyya da kuma yadda za a tabbatar da an yi zabe na gaskiya.