Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alkali, ya musanta rade-radin da ke yawo cewa Rundunar ’Yan Sandan Najeriya na shirin dawo da sashen ’yan sandan SARS, bayan rushe ta da aka yi a shekarar da ta wuce.
An rushe sashen SARS mai yaki da ayyukan fashi ne a watan Oktoban 2020, bayan tarzomar #EndSARS da aka gudanar a sassa daban-daban na kasar nan.
- Shin za a hana yara mallakar waya a Najeriya?
- Neman hana ’yan shekara 17 sayen layin waya ya yamutsa hazo
Bayan rushe SARS an kafa wani sashen ’yan sandan mai suna SWAT, domin maye gurbin ayyukan SARS.
Sai dai a ranar Alhamis wasu rahotanni sun bayyana cewa tuni aka fara shirye-shiryen dawo da SARS, shekara guda bayan rushe ta da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi.
Sai dai shugaban ’yan sanda, cikin wata sanarwa da kakakin ’yan sanda na Najeriya, Frank Mba, ya fitar ya musanta rahotannin.
Baba ya ce babu wani yunkuri ko shiri da suke yi na sake dawo da SARS bakin aiki.
“Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta samu labarin wasu rahotanni da ke ta yawo cewa ana shirin dawo da SARS.
“Ina so na tabbatar wa jama’a cewa babu wani abu mai kama da hakan, an rushe SARS kuma sun tafi ke nan babu wani abu da zai sa su sake dawowa.
“An gama shirye-shiryen yadda sabuwar tawagar ’yan sanda za su fara aiki don maye gurbin da SARS ta bari.
“Yanzu muna shirin kawo wadanda za su yi aiki kan tsari da bin doka da oda kamar yadda aka tanadar.
“Don haka ana jan hankalin jama’a da su yi watsi da wannan labari wanda babu gaskiya a cikinsa,” a cewar sanarwar.