✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba mu da sha’awar daukar Cristiano Ronaldo —Lobi Stars 

Kungiyar ta ce tana yi wa Ronaldo fatan alheri, amma ba za ta iya zawarcinsa.

Kungiyar Kwallon Kafa ta Lobi Stars da ke garin Markudi a Najeriya, ta bayyana cewar ba ta da sha’awar daukar Cristiano Ronaldo wanda ya raba gari da Manchester United.

Kungiyar da ke garin Markudi a Najeriya, ta sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da fitar a shafinta na Intanet.

Sanarwar ta ce: “Mu Lobi muna sanar da cewar ba mu yi wani yunkuri na tuntubar Cristiano Ronaldo ko kuma wakilansa ba.

“Muna masa fatan alheri.”

Yanzu haka dai Ronaldo ya mayar da hankalinsa ne kan Gasar Kofin Duniya da ake bugawa a Kasar Qatar.

Manchester United ta warware alakar da ke tsakaninta da dan wasan bayan wata hira da ya yi da dan jarida Piers Morgans, inda ya caccaki kungiyar da mai horas da ita, Erik ten Hag.