Rundunar ’yan sanda a Jihar Kaduna ta ce ba ta da labarin sace mambobin cocin RCCG (Redeemed Christian Church of God) da aka yi a kan hanyar Kachia da ke Jihar.
Aminiya ta ruwaito yadda wani Eje Kenny Faraday ya wallafa hotunan motar da ake zargin an yi garkuwa da mutanen cikinta a ranar Juma’a.
- An kwaso ’yan Najeriya 255 da suka makale a Saudiyya
- Ya kamata a dauki matasa 50m aikin soji —Tinubu
- Buhari ya taya Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwa
- Taron Tinubu: An tsaurara tsaro a Gidan Gwamantin Kano
Faraday ya bayyana cewa da kyar ya sha yayin da aka sace wasu mambobin cocin RCCG da ke cikin motar.
Rahotanni sun bayyana cewa mambobin sun taso ne daga garin Kaduna zuwa yankin Kafancan da ke Karamar Hukumar Jema’a don gudanar da harkokin da suka shafi cocin.
Faraday ya wallafa cewa “Dukkanin fasinjojin an yi garkuwa da su a garin Kachia mai tazarar kilomita 63 da cikin birnin Kaduna.
Sai dai yayin da aka tuntubi kakakin ’yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, ya ce ba su da rahoton faruwar lamarin.
Jalige, ya kara da cewa rahoton ofisoshin ’yan sanda Kachia, Kasuwar Magani da Kajuru bai bayyana an sace mutane a yankin ba.
Ya bayar da tabbacin cewa rundunarsu za ta ci gaba da bincike don gano hakikanin gaskiyar lamarin.