✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu amince a dawo da Rahama Sadau ba-MOPPAN

Shugaban Kungiyar Masu Shirya Fina-Finan Hausa (MOPPAN), Alhaji Kabiru Mai Kaba ya ce ba su yarda da matakin da Hukumar Tace Fina-Finai ta dauka kan…

Shugaban Kungiyar Masu Shirya Fina-Finan Hausa (MOPPAN), Alhaji Kabiru Mai Kaba ya ce ba su yarda da matakin da Hukumar Tace Fina-Finai ta dauka kan yafewa Rahama Sadau ba.

Kabiru Maikaba ya yi wannan bayanin ne bayan Shugaban Hukumar Tace-Tacen, Isam’ila Afakallah ya yi jawabin cewa sun yafewa jarumar, sannan kuma a shirye suke su ci gaba da tace fina-finan da ta fito a ciki, ko kuma ta xauki nauyi.