✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba magani a asibitin fadar shugaban kasa-Majinyata

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano cewa marasa lafiya asabitin fadar shugaban kasa suna kukan karancin magunguna da kayan aiki a asibitin. An…

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano cewa marasa lafiya asabitin fadar shugaban kasa suna kukan karancin magunguna da kayan aiki a asibitin.
An gina asibitin ne don a rika lura da shugabannin Najeriya da mataimakansu da kuma iyalansu tare da ma’aikatan fadar shugaban kasar.
Majiyoyin da ke asibitin sun bayyana cewa  rabon da a kawo magunguna  asibitin tun watan Afrilun shekarar da ta gabata.
Akwai korafe-korafe kan karancin magunguna kamar faracitamol da bitamin B da auduga da sirinjin allura.
Lamarin ya rika sanya fargaba ga majinyata don lokacin da wakilinmu ya ziyarci asibitin, ya tarar marasa lafiya bakwai ne ke son ganin likita.