✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ma neman bashin kudi daga Bankin Duniya – Ministar Kudi

Ministar Kudi Misis KemiAdeosun ta ce gwamnatin tarayya ba ta mika bukatar neman bashin kudi ga Bankin Duniya da kuma Bankin Raya kasashe na Afirka…

Ministar Kudi Misis KemiAdeosun ta ce gwamnatin tarayya ba ta mika bukatar neman bashin kudi ga Bankin Duniya da kuma Bankin Raya kasashe na Afirka ba tukuna, kamar yadda jaridar Financila Times ta ruwaito a ranar Lahadi.
Mai Ba Ta Shawara ta Fuskar Yada Labarai Mista Festus Akanbi ya ce Najeriya ba ta nemi wani bashi ba. Daga nan sanarwar ta ruwaito ministar tana cewa: “Maganar gaskiya nan ita ce kasafin kudin bana yana gaban majalisa, kodayake akwai bukatar da ake da ita na aro kudi don cike gibin kasafin kudin har Naira tiriliyan daya da biliyan takwas don aikin raya kasa.”
A karshe ta ce gibin za a cike shi ne ta hanyoyin da suka dace daga ciki da wajen kasar nan. Ta ce kasar nan tana duba yiwuwar tuntubar Bankin Duniya da kuma Bankin Raya kasashe na Afirka saboda rangwaman kudin ruwan da suke dorawa.