Alamu na nuna cewa ba lallai ne wa’adin da Gwamnatin Tarayya ta tsayar na sake bude filayen jiragen sama ranar Litinin, 21 ga watan Yuni ba, la’akari da irin shirye-shiryen da hukumomin sufurin jiragen suka yi.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin ke cewa ba gaggawa take yi ba wajen sake bude filayen.
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ya bayyana haka yayin wani taron karawa juna sani na masu ruwa da tsaki kan harkar sufurin da ya gudana ta bidiyo a ranar Talata.
Taron wanda Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta shirya ya mayar da hankali kan tsare-tsaren sake bude harkar sufurin nan ba da jimawa ba.
- Za a bude filayen jiragen sama biyar
- An tsawaita dokar hana sufurin jiragen sama a Najeriya
- Coronavirus: Gwamnatin Najeriya ta rufe filayen jiragen sama
A kwanan nan ne dai kwamitin Kar-ta-kwana da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar coronavirus ya ce mai yiwuwa a sake bude filayen a ranar 21 ga watan Yuni, bayan shafe kimanin watanni uku a rufe sakamakon bullar cutar.
Shi dai kwamitin tsara bude sufurin jiragen saman wanda Babban Daraktan NCAA, Kyaftin Musa Nuhu ke jagoranta ya jima yana tattaunawa da masu ruwa da tsaki, musamman kamfanonin jiragen kan yadda za a dawo da harkar ka’in da na’in.
Akalla kamfanoni shida ne cikin 14 ya zuwa yanzu suka shirya dawowa aiki gadan-gadan bayan kammala yi wa jiragensu feshin kwayar cuta, kamar yadda Daraktan Sashen Kula da Lafiyar Jirage na NCAA, Ita Awak ya bayyana.
To amma yiwuwar sake bude filayen ranar Litinin din za ta ta’allaka ne kan bayanin da Babban Baraktan NCAA zai yi wa kwamitin kar-ta-kwanan ranar Juma’a.
Da yake jawabi yayin tattaunawar wadda babban jami’in kwamitin na kar-ta-kwana, Dr Sani Aliyu ya samu halarta ya ce an sami nasarori da dama a yunkurin dawo da harkar sufurin, ko da yake ya nuna kokwanton cewa zai yi wuya a iya kammala ragowar tsare-tsaren da ba’a iya kammalawa ba a baya cikin kwanaki hudu masu zuwa.
Ya ce la’akari da irin shirye-shiryen da aka yi zuwa yanzu, zai yi wuya a iya dawo da harkar nan da ranar Litinin.
Ministan ya ce matukar za a sake bude filayen ranar Litinin, to dole a tabbatar da samar duk kayayyakin kariyar da ake bukata a cikinsu.
Shi kuwa a nasa bangaren Dabban Daraktan na NCAA, ya ce ranar Juma’a ce za a tantance ko za a bude filayen ranar Litinin ko a’a.
A cewarsa, “A matsayina na shugaban kwamitin sake bude filayen, akwai jan aiki a gabana. Gobe [Juma’a] ne zan mika rahoton wucin gadi wanda kuma shi ne zai fito da hakikanin halin da ake ciki.
“Idan ba mu shirya ba, za mu yi bayani karara, saboda ba za mu yi abin da za mu zo muna da-na-sani ba daga baya”, inji shi.