Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta sanar da cewa babu gudu babu ja da baya dangane da zanga-zangar gama-gari da za ta gudanar a ranar 27 da 28 ga wannan wata na Fabarairu.
Sanarwar dai martani ce ga Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS)da ta bukaci kungiyar kwadagon ta sauya tunani kan zanga-zangar da a cewarta babu lallai ta wanye lafiya ba.
- Tinubu ya naɗa Kemi Nanna Nandap shugabar hukumar shige da fice
- An bai wa kowanne gwamna N30bn ya rage tsadar rayuwa a jiharsa — Majalisar Dattawa
Aminiya ta ruwaito cewa a safiyar wannan Larabar ce DSS ta yi kira ga kungiyar kwadagon da ta jingine shirinta na gudanar da zanga-zanga domin ci gaba da wanzuwar zaman lafiya da walwalar jama’a.
Gargadin DSS na zuwa ne tun bayan da a Juma’ar da ta gabata, NLC ta ayyana zanga-zangar kwanaki 2 a fadin kasar nan kan halin matsin da ‘yan Najeriya ke fuskanta da kuma matsalar tabarbarewar harkokin tsaro a fadin kasar.
Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawunta, Peter Afunanya ya fitar, DSS ta bukaci bangaren ‘yan kwadagon ya bi tafarkin tattaunawa a maimakon hanyoyin daka iya kara yamutsa hazo.
Sanarwar ta kara da cewar gwamnatoci a dukkanin matakai na iya bakin kokarinsu wajen rage radadin halin kuncin da ake ciki, don haka ya kamata a kyautata musu zato.
Sai dai da ya ke martani kan wannan gargadi na DSS, Shugaban NLC Joe Ajaero, ya ce maimakon yi wa kungiyarsu barazana, kamata ya yi DSS ta daura damarar kama duk wadanda za su kawo hargitsi a yayin zanga-zangar.
A cewar Kwamared Ajaero, tarihi ba zai taba yafe wa ƙungiyar ƙwadago ba ma damar ta zauna ta yi shiru kuma ta nade hannu alhali ’yan Najeriya na ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa ba.
Shugaban kungiyar kwadagon, wanda ya bayyana matakin da ke tafe a matsayin “zanga-zangar lumana kan tsadar rayuwa da ba za a lamunta ba,” ya kara da cewa kungiyar kwadagon ba za ta nade hannunta ba yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da rayuwa cikin kunci.
“Muna so DSS ta sani cewa babu inda aka taba samun tashin hankula a zanga-zagar lumana da kungiyar kwadago ta taba gudanarwa, don haka batun mu janye wannan bai taso ba.”
Shugaban NLC ya koka kan yadda tattalin arzikin kasar ya tabarbare yana mai cewa yanzu haka darajar naira ta kara kundunbala inda farashinta a kasuwar canjin kudi ya kai N1,900 kan kowacce dalar Amurka daya.
Ya ba da tabbacin cewa babu wanda ya ke son ci gaban Najeriya kamar kungiyar kwadago kuma ba za ta taba yin wani abu da zai jawo rashin zaman lafiya ba.