✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba domin zama attajiri ake aikin jarida ba – Buhari Auwalu

Malam Buhari Auwalu, babban ma’aikacin Gidan Rediyon Najeriya na Kaduna ne. Ya taba zama wakilin gidan a fadar Shugaban kasa, kuma shi ne wanda ya…

Malam Buhari Auwalu, babban ma’aikacin Gidan Rediyon Najeriya na Kaduna ne. Ya taba zama wakilin gidan a fadar Shugaban kasa, kuma shi ne wanda ya kirkiro shirin nan mai farin jini mai suna, Oscar. A hirarsa da Aminiya, ya bayyana yadda ya fara aikin jarida da wadansu al’amuran da suka shafi aikin da sauransu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinka?
Buhari Auwalu: Assalamu alaikum sunana Buhari Auwalu. An haife ni a ranar 28 ga watan Yuni, 1956 a wani kauye da ake kira Anchau Taka Lafiya a karamar Hukumar Kubau da ke Jihar Kaduna. Na fara karatun allo da na addini a can, amma dalilin sauya wa mahaifina wurin aiki, sai muka koma garin Ikara, a can ne na fara karatun firamare a shekarar 1961. Har ila yau, da aka kara sauya masa wurin aiki zuwa Sabon Garin Zariya, wannan ya sa na kammala karatun firamarena a Sabon Garin Zariya.
A 1968 na wuce Kwalejin Alhudahuda da ke Zariya, inda na kammala a 1973. Da sakamakon ya fito sai aka yi rashin sa’a nawa bai yi kyau ba. Abin ya ba ni mamaki, amma sai na zabi in sake maimaita shekara guda. Ban yi hakan a wannan makaranta ba sai na tafi Kwalejin Horar da Malamai ta Basawa wato (Basawa Teachers’ College). Bayan na kammala nan ne sai na zama shugaban makarantar firamare.
Lokacin da aka bude Kwalejin Horar da Malamai ta garin Kafanchan, sai na nemi aiki a can, amma bayan fitar da sunayen wadanda suka yi nasara, sai ban ga nawa ba. Amma da na duba na ga duk wata cancanta da aka zayyana ai ina da ita. Sai na rubuta takardar korafi wato (Petition Letter) zuwa ga Gwamnatin Jihar Kaduna, a lokacin Gwamna Gurof Kyaftin Usman Jibril ne. Aka ba ni amsa kuma aka sake sabon lale, inda aka kara tantance mu duka, amma har ila yau ban samu ba, domin wannan kara da na kai, kuma abin na ma’aikatar ilimi ce. Amma fa sai da aka zubar da kusan rabin wadanda aka dauka, domin a takardar da na rubuta na bayar da misalai har da wadanda ba su halarci tantancewar ba.
A 1975 na wuce Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda na yi Difloma a fannin harshen Hausa. Bayan haka sai na kara dawo wa fannin koyarwa. Ina cikin haka ne sai na ga Kwalejin Horar da Manyan Hafsoshin Soji ta kasa wato (NDA) tana neman masu sha’awar aikin soja. Sai na sayi fom, na rubuta jarrabawa kuma aka kira ni. Saboda ni ma’abocin karance-karancen jarida ne, sai kuma na ga ana neman ma’aikata a Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna (FRCN). Sai na ce ni ban san kowa ba, amma sai dai na rubuta takardar neman aiki, na aika. Bayan haka, sai (NDA) suka aiko cewa na yi nasara. Hakazalika FRCN. Ashe kuma ni ban sani ba, akwai wani kawuna shi kuma ya nema mini aiki a ma’aikatar kudi.  Allah cikin ikonSa Ya sa na samu duka. Ka ga ina da zabi uku ke nan: ko dai na je aikin soja, ko aikin rediyo, ko kuma ma’aikatar kudi, domin ita takardar aikinta ma har da na kwas zuwa wata makaranta a garin Ilorin.  Kuma ni mutum ne mai sha’awar karo karatu. Amma sai na duba na ga cewa ina da kanne. A lokacin mun dogara ga Allah kuma da mahaifiyarmu, domin mahaifinmu Allah Ya yi masa rasuwa lokacin da nake aji biyu na makarantar sakandare. Sai na yanke shawarar bari in kama aiki domin kannena su tafi makaranta. Sai na zabi aiki da FRCN Kaduna, inda na fara aiki a watan Satumbar shekarar 1977.
Aminiya: Da wane shiri ka fara aiki a FRCN Kaduna?
Buhari Auwalu:  A lokacin idan aka dauke ka aiki a wani fanni na gidan rediyon ba za ka fara aiki ba nan take. Za ka fara aikace-aikace ne a wadansu fannoni na daban da ke gidan. Ka ga an dauke ni aiki ne a bangaren sashen labarai da al’amuran yau da kullum. To amma sai da na fara koyon aiki a bangaren shirye-shirye, inda aka koya mini yadda ake gabatar da shirye-shirye da tsara su da sauransu. Har ila yau, sai an koya maka yadda ake sarrafa na’ura.
Bayan haka sai  na dawo bangarena. A nan kuma ina aiki biyu ne, wato aikin fassara labarai da kuma mai aiko da labarai wato (Reporter).
Aminiya: Wadanne kalubale ka fuskanta wajen aikin fassara musamman yadda ka taba zama mai fassara jawabin shugaban kasa?
Buhari Auwalu:  Na fara wannan aikin ne lokacin da aka dawo da Babban Birnin Tarayya Abuja daga Legas. Yadda na gudanar da aikin shi ne Shugaban kasa idan zai yi jawabin kasafin kudi ana dauka ne a kaset daga baya sai a sanya wa jama’a domin sauraronsu. Bayan an kammala haka ne sai a ba mu jawabin a rubuce. Kuma watakila ba zai kai hannuna ba sai karfe 10:00 ko 1:00 na dare, kuma ana bukatarsa washegari da safe. Da zarar ya zo hannuna sai na wuce ofis, wani lokaci haka zan kwana fassara jawabin har zuwa akalla karfe 5:00 na safe. Saboda yadda ake yi shi ne, sai ka fara karanta shi gaba daya domin ka fahimta kafin ka fara fassarawa. Kuma yawancin aikin da na yi lokacin mulkin Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ne, wanda ba ya gajeran jawabi. Yakan yi jawabinsa ne daga shafi 70 zuwa sama. Idan ina aikin sai in ga wata kalma da ban fahimce ta ba, to fa sai na bukaci karin haske daga wani jami’in gwamnati. Bayan na kammala kuma, sai na bugo waya Kaduna. Sai na karanto shi domin a nada. Daga nan sai a sanya shi a daidai lokacin da za a sanya jawabin Shugaban kasa a sashen Inglishi domin su tafi tare da fassarar da na yi.
Aminiya: Daga yaushe ka zama wakilin FRCN a Fadar Shugaban kasa
Buhari Auwalu: An fara tura ni Jihar Sakkwato ne a shekarar 1981, daga nan aka koma da ni Jihar Kano, inda a cikin shekarar 1987 ne aka yi mini sauyin wurin aiki daga Jihar Kano zuwa Abuja. Amma a lokacin Shugaban kasa yana Legas ne. Saboda haka muna nan Abuja ya zo ya same mu.
Aminiya: Me za ka iya tunawa lokacin da marigayi Janar Sani Abaca ya karbe mulkin kasar nan daga hannun Shugaban Gwamnatin Rikon kwarya Ernest Shonekan?
Buhari Auwalu: Wato abin da ya faru shi ne, lokacin Janar Abaca yana Legas, a matsayinsa na Babban Hafsan Tsaro.  Mu dai mun fahimci cewa kasar ba ta da lafiya, saboda lokacin idan Mista Shonekan ya kira gwamnonin kudancin kasar nan taro ba sa zuwa domin ba su yarda da shi ba. Wata rana sai muka ga manyan sojojin suna taruwa a nan Fadar Shugaban kasa. Ganin haka mu kuma sai muka karasa ciki saboda mun san cewa akwai labari.  Ana cikin wannan hali har zuwa tsakar dare ba wani abu. A karshe lokacin da suka watse ba a bayyana mana komai ba. Amma ni na lura da wani abu, abin da na lura da shi kuwa shi ne: Motar da Janar Abaca ya fito daga ciki tana dauke da tuta biyu ne, guda ta kasar nan, guda ta sojoji. Kuma idan ban da Shugaban kasa babu wanda ke samun hakan. Ni ban fada wa kowa ba, sai na ce a zuciyata watakila an samu sabon Shugaban kasa.
Aminiya: Me ne dalilin kirkiran shirin Oscar wanda a baya kake jarogarantar gabatarwa?
Buhari Auwalu: A gaskiya na fara shirin Oscar ne tun lokacin ina Kano, amma lokacin bai da suna. Kuma dalilin kirkiransa kuwa shi ne, akwai wani lokaci da aka baza jita-jita cewa an kama Alhaji Halilu Getso wanda yana daya daga cikin ’yan jaridan da suka yi wata hira da Shugaban kasa na wancan lokacin wato Janar Muhammadu Buhari, inda aka ruwaito shugaban yana cewa idan Najeriya ba ta da kudin da za ta bai wa alhazai, to ta yiwu aikin hajjin akwai wasu ’yan matsaloli. To ina Kano sai aka baza jita-jita an kama ’yan jaridan da suka yi wannan tattaunawar da shugaban kasa. Mu kuma mun kwana da sanin ba a kama su ba. Shi ke nan ka san akwai wasa tsakanin Kanawa da Zage-zagi, sai na ce lallai Kanawan nan mutane ne masu son mu’amala da jita-jita. Saboda haka sai na rubuta shagube a kan an kama Halilu kaza-kaza, a karshe sai na ce duka wannan jita-jita ne.  Na aiko ga shirin da Halilun ke yi na Alkawari Kaya ne. Aka sanya a shirin, inda shi ma ya yi sharhi ya ce Buhari ya dauki Kanawan mutanen da bai saba da su ba.

Na sanya wa shirin suna ne lokacin da nake Abuja, inda na rada masa suna Oscar. Kuma yadda aka yi na sa masa suna shi ne wata rana ina kallon wani shiri irin na namun daji a talabijin. Sai aka nuna wata tsuntsuwa, ta yi kwai, tana kwanci. Sai ta tafi neman abinci, kuma kafin ta dawo sai daya daga cikin kwayayen ya kyenkyeshe kansa. Sai mai bayar da labarin yake cewa tsuntsuwar ta tafi ba ta dawo ba, amma dan tsako Oscar ya kyenkyeshe kansa. Shi ke nan sai na ce wannan sunan zai dace da sabon shirina domin da ya fito ya yi ta karambani ya je nan, ya je can. Har ila yau, yana da kyau jama’a su fahimci cewa a lokacin muna samun labaran gwamnati wadanda jama’a ba su san da su ba. Kuma ba shi yiwuwa mu fade su a labarai saboda tsaron lafiyarmu da zaman lafiyar kasa da sauran dalilai. Kuma dole mu samu hanyar da za mu bayyana wa mutane wadancan labaran. Saboda ko da misali na bayar a cikin shirin, misali ne na zahiri. An dai rurrufa ne saboda nakan lura da dokokin aikin jarida ta yadda ko an kai ni gaban shari’a ba za a kama ni da laifi ba.
Aminiya: Wane irin martani ka samu daga hukumomi game da shirin?  
Buhari Auwalu: Na taba samun labari daga baya saboda muna da abokai a cikin jami’an tsaro, inda aka fada mini cewa an yi shirin a kama ni sau fin shurin masaki, amma abin da ya sa ba a kama ni ba shi ne saboda ana ganina da darakta wane, ana tsammanin wasu maganganun da nake yi gwamnati ce ke ba ni umarnin in bayyana su domin ta ji ra’ayin mutane. Amma daga bayanan da na samu a lokacin masu sauraron shirin suna jin dadin shirin sosai.
Aminiya: Me ya sa ka kara dawo da shirin a kwanakin baya?
Buhari Auwalu: Eh, a’a. Wato shugabanni na da ga alama sun fi hakuri. Na dan dawo da shirin, amma kuma sai na lura cewa shugabannin yanzu suna da karancin hakuri. Kuma saboda sha’anin siyasa da sauransu ya sa wani lokaci sai na dakatar da shi.
Aminiya: Akwai wadansu kasashe da ka taba ziyarta?
Buhari Auwalu: Eh, na je kasashe kamarsu: Saudiyya da Ingila da Amurka da Senegal da sauransu.
Aminiya: Bayan shirin Oscar akwai wadansu shirye-shiryen da ka gudanar a FRCN?
Buhari Auwalu: Akwai shirye-shirye kamarsu: ‘Da Bazarku Ake Rawa’ da ‘Jakar Magori’ da ‘Barka da Yau’ da kuma ‘Afirka a Makon Jiya’. Amma akwai wani shirin da na kirkiro shi mai suna ‘Kowa ya Dade a Bayi Zai ga kuda da kaho’, wanda yake magana a kan rayuwar Musulmi a kasar Amurka. Kuma a gaskiya na fi kaunar shirin ‘Oscar’ da kuma ‘Kowa ya Dade a Bayi Zai ga kuda da kaho’.
Aminiya: Kana da wani kira kan yadda za a kara inganta aikin jarida?
Buhari Auwalu: Ya kamata masu kafofin yada labarai su kyautata yanayin aikin ma’aikata. Matasa ’yan jarida kuma na fahimci kamar sun kosa ne su yi kudi. A aikin jarida kuwa ba a yin kudi. Ba aiki ne na sai an yi kudi ba, za dai a san ka, amma idan kana so ka yi kudi ne, to gara ka nufi kasuwa.
Aminiya: Wadanne abubuwa ne ba za ka manta da su a tarihin aikinka ba?
Buhari Auwalu: Akwai su da dama, amma wanda zan tuna su ne: Maganar kama wata mata mai suna Gloria Ukoh da hodar ibilis a Kano a kan hanyarta ta zuwa birnin Landan. Wannan ya jawo zarge-zarge, domin a gaskiya ba zan iya bayyana abin da na sani ba yanzu, saboda an sato wadansu takardu na sirri kuma na gani, wadansu masu hannu a ciki  suna nan da ransu. Abu na biyu shi ne, wata rana lokacin ina Abuja na kira wani na kusa da marigayi Janar Shehu Musa ’Yar’aduwa bayan na samu wadansu bayanai, nake shaida masa cewa don Allah ni bai san ni ba, kuma ban da wata hanya da zan kai gare shi kai-tsaye. Amma ya yi kokari ya bayyana wa Janar Shehu cewa idan ba sa’a aka yi ba wani abu zai same shi a wannan dare. Ya ce mini zai fada masa. Shi ke nan, washegari da safe karfe 7:00 ba ta karasa ba. Sai wannan da na bai wa sakon ya yi sallama a kofar gidana.  Sai ya ce Wallahi an kama Shehu a jiya, sai na ce ba ka fada masa ba ne. Sai ya ce Wallahi ya manta ne bai gaya masa ba, saboda wani taron siyasa da suka shiga a daren. Kamun da bai dawo ba ke nan.
Aminiya: Ya batun iyali fa?
Buhari Auwalu: Ina da mata biyu da ’ya’ya da dama. Har ila yau, na yi ritaya daga aikin jarida ne a shekarar 2012, inda na koma gida Zariya da zama. Daga baya FRCN ta kara bukatar aikina, ka ji yadda na dawo FRCN Kaduna a matsayin shugaban bangaren labarai da al’amuran yau da kullum.