✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba dole ne Najeriya ta ci gaba da zama kasa daya ba – Kingibe

Ya ce hatta aure tsakanin mata da miji ana iya datse igiyarsa in akwai rashin jituwa.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Ambasada Babagana Kingibe, ya ce ba dole ne Najeriya ta ci gaba da zama dunkulalliyar kasa daya ba.

Babagana, wanda kuma shi ne wakilin Najeriya a kasar Chadi na wadannan kalaman ne ranar Asabar a wajen taron bayar da kyaututtuka da kamfanin jaridar The Sun ya shirya a Legas.

A cewarsa, hatta aure tsakanin mata da miji ana iya datse igiyarsa in akwai rashin jituwa, ballantana ci gaba da zama kasa daya.

Sai dai ya tunatar da masu yunkurin ballewa daga kasar cewa ba lallai ne hanyar da suke bi ta bulle da su ba.

Ya ce, “An haifeni a Najeriya, na girma na yi karatu a cikinta, kuma na yi amanna da ita. Haka duk sa’o’ina sun yarda da ita, mun yarda cewa ba mu da wani wurin da ya wuce ta.

“Sai dai na san akwai wasu daga cikin sa’o’ina da ke tunanin ba zai yuwu a tattauna makomar Najeriya ba, amma ni ina ganin za a iya yi saboda ba dole ba ne ta dauwama a matsayin kasa daya. Hatta aure ma akan iya kawo karshensa tsakanin mata da miji.

“Daga lokacin da wani daga cikin wadanda ke cikin kasa ya ji zamansa cikinta ba shi da wani amfani a wajensa, kamata ya yi a ba shi dama ya kama gabansa.

“Idan mutum ya ce yana son ballewa, ina fatan ya san me hakan ke nufi, ba wai fadin kasar za a yanka a basu su dauka su kai kasar Ghana ba alal misali, dole a nan za ta ci gaba da zama, su ma haka.

“Kira na ga kowa shi ne kamata ya yi mu rika girmama juna da ra’ayoyin wasu, ba wai tozarta juna ba,” inji shi.

Babagana wanda kuma ya karbi kyautar ‘Cimma Nasara a Rayuwa’ da jaridar ya kuma tunatar da masu son ballewa daga Najeriya da su tsaya su yi nazarin asara da ribar da ke tattare da yin hakan.

%d bloggers like this: