✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba dan majalisar da ke kwashe wa Buhari kafa – Lawal Shu’aibu

Sanata Lawal Shu’aibu shi ne Shugaban Jam’iyyar APC shiyyar Arewa a tattaunawarsa da Aminiya, ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa sanatoci da ‘’yan majalisa…

Sanata Lawal Shu’aibu shi ne Shugaban Jam’iyyar APC shiyyar Arewa a tattaunawarsa da Aminiya, ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa sanatoci da ‘’yan majalisa suna kwashe wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kafa:

Aminiya: Me za ka ce kan zargin da ake yi cewa ’yan majalisar dattawa da ta wakilai ba sa tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari?
Lawal Shu’aibu: Ba gaskiya ba ne, babu dan majalisar da ba ya tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, duk wanda ya ce haka ba gaskiya ba ne. Surutai ne dai na mutane saboda su kawo rashin jituwa a jam’iyyarmu ta APC, amma mun san kowane dan majalisa in dai dan APC ne yana tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Aminiya: A yanzu wane shirye-shirye Jam’iyyar APC ke yi don ganin ta cika alkawurranta ga ’yan Najeriya?
Lawal Shu’aibu: Eh to, idan aka tsaya aka duba ai watanmu uku, cikin watan nan uku in an duba za a ga abubuwan da muka fara, mu gwamnati ne wadda tun muna jiran gado ake kokarin a shirya yadda za a tafiyar da al’amarin kasar nan da kuma yadda za a mika mana gwamnatin. Mun shirya namu kwamiti su ma sun shirya nasu, amma sun ki bari a zauna, su mika gwamnati a hannun namu kwamitin.
To muka zo har aka rabu da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, ba a mika mana komai ba, wannan kuma ai kin ga babban aiki ne, kuma in an tsaya an duba, babu abin da Shugaba Buhari ke yi in ban da kowace ma’aikata sai ta yi masa bayanin yadda abubuwa suka kasance a wannan  ma’aikata. Kuma bai da niyyar ya bar kowace ma’aikata, sai sun zo sun yi masa bayanin abubuwan da suka yi kuma sai sun ba shi a rubuce, duk ya harhada komai da komai, kafin ya yi haka ba yadda za a yi a ce ya nada ministoci ya tura su ma’aikatun da shi kansa bai san abin da suke ciki ba.
Tunda ba wanda ya ba shi, to abin da muke kokarin yi ke nan don samun ci gaban wannan kasa tamu mai albarka Najeriya. Idan muka lura akwai wasu wurare, da in aka ga misali an tafka kuskure nan take sai Shugaban kasa ya ce a gyara, kamar zama a gurbin da bai cancance ka ba, sai ya ce ka sauka ka je inda ya kamata ka yi aiki, idan kuma wani ya je ya tafka shirme da zai shafi mutuncin kasa ana iya dakatar da shi, duk wannan ba a cewa sai an gaya wa Shugaban kasa. Kowa da bangaren da ya kware a kan aiki, kamar jami’an tsaro su ma suna da nasu aikin, Shugaban kasa ya fi maida hankali ne a kan sha’anin tsaro, duk duniya kowa ya ga abin da ya yi.
Aminiya: Jam’iyyarku ta APC ta samu nasarar hawa karagar mulki saboda mutane na dokin canji, ga shi har yanzu wasu na kuka da rashin ganin hakan, ko me ya sa haka?
Lawal Shu’aibu: Ba yadda za a yi a ga canji, sai in ka tabbata ga yadda abu yake da za ka canja, duk abin da ake fada jita-jita ne kawai, Shugaban kasa so yake ya samu zahirin, ya tabbatar ga abin da muke ciki, sannan ya kawo canjin da ake bukata, amma kuma duk wani canji ya fi irin duk wanda aka kama ya yi rub-da-ciki da dukiyar gwamnati, a ce maza-maza ya dawo da su? Da haka za a samu a yi tattalin arzikin kasar nan kamar yadda ya kamata, kuma wannan aikin da muke yi babu gwamnatin da aka yi.
Aminiya: Shin kuna ganin jam’iyyarku ta APC, ta hannun Shugaba Buhari za ta yi tasiri wajen yaki da almundahana, ko yaya kuke ganin za ku iya kawo kan lamarin?
Lawal Shu’aibu: Wato ba gwamnati ke kama mutane ba, da can in sun yi yunkurin kamawa, saboda waccan gwamnatin ta PDP gwamnati ce da ba ta yarda a kama mutum ba, saboda ba su yarda da daukar kudin gwamnati sata ne ba. Mu kuma mun yarda cewa sata ne, su jami’an tsaron nan wato suna jin tsoron su je su kama masu laifi irin wannan, to sai ya zama aka wayi gari kowa yana ta abin da ya ga dama, saboda sun san ko sun kama za a sake su.
Mu kuma da muka zo, Shugaba Buhari ya ce kowa ya je ya yi aikinsa. Shi ya sa yau suke aikinsu, babu wanda Shugaban kasa ya ce a kama, amma su jami’an tsaro sun san aikinsu, sun san wanda ke da laifi da za su kama a tuhume shi, kuma babu rangwame ga duk mai laifi, da haka za a fitar da gurbatattun ma’aikata a kafa masu gaskiya da yin adalci, kasa ta gyaru.
Aminiya: Jam’iyyar PDP na cewa akwai munafunci a tafiye-tafiye da Shugaba Buhari ke yi a kasashen Afirka, me za ka iya cewa kan wannan?
Lawal Shu’aibu: Abin da ya kai Shugaba Buhari kasashen Afirka, na farko ya nemi hadin kai da duk kasar da take da mawabta da Najeriya. Shi ya sa ya ziyarce su don a taimaka a hada kai a yaki ’yan ta’addan Boko Haram, don haka in ya zauna kamar yadda tsohon Shugaban kasa ya zauna, ba za mu cimma nasara ba wajen kawo karshen wannan bala’in da ya addabi kasarmu ba. Yanzu kowa ya san cewa ko Maiduguri an dan samu walwala, ba wai gaba daya an gama da su ba ne, amma an samu saukin gaske, wato a ce cikin tafiya ta mil dari an yi mil saba’in da wani abu.
Aminiya: Akwai masu ganin Jam’iyyar APC ta kasa tafiyar da kasa yadda ya kamata, me za ka ce?
Lawal Shu’aibu: Eh, to, mun ka sa din, don mun ki yin yadda wadanda suka bar mulki suke yi. Siyasa ce kawai, a kago wannan, a kago waccan don a samu a bata mana suna. Amma abin da nake so irin wadancan mutane su gane shi ne da jama’ar kasar nan sunyi maraba da irin aikin da suke yi ai da ba a canza su ba. Mu abin da muke yi shi ne, muna son mu tabbatar da cewa mun cika duk alkawarin da muka dauka a lokacin da muke takara, tunda muka karbi gwamnati daga hannunsu ba yadda za a yi su so duk wani abu da muke yi, komai kyaunsa. Muna tattalin gyaran kasar nan kuma jama’a sun san muna yi.
Aminiya: Kuna ganin Shugaba Buhari zai iya ceto ’yan Chibok da ’yan Boko Haram suka sace?
Lawal Shu’aibu: Insha Allahu in suna raye sai an kwato su an maida su wurin iyayensu, wato saboda karfin mulki ya dawo hannunmu babu wanda ya san abin da ake ciki, ai kafin Shugaban kasa ya ce su wadancan jami’an tsaro na sojoji kafin ya sallame su, sai da ya zauna ya yi aiki da su, sai da suka yi masa bayani, ga abubuwan da suka samu, ga abubuwan da suka yi. Da ya gane duk zancen banza suke yi, sai ya ce musu, to ya gode, sai ya sallame su, sai ya saka nasa, kuma ya ce to, ga abin da wadancan suka gaya masa amma ku je ku yi naku, na ba ku adadin lokaci kaza, harkar Boko Haram a san cewa an maida shi tarihi.
Aminiya: Kuna ganin akwai tabbacin cewa za su iya aikin ke nan?
Lawal Shu’aibu: kwarai da gaskiya, saboda Shugaban kasa ya ba su hanyoyin da za su bi su ciwo kan wannan lamari, ai da can abin da ake yi shi ne, idan aka dauki kudin sojojin da aka tura Gombe da Yobe da Adamawa da Borno a nan Abuja ake rabe kudin ba sa kaiwa gare su. Makamai in aka ce a saya za a fitar da kudin makaman amma ba a saye, sai a rabe kudin, sai ka ga sojojin Najeriya da sun ga ’yan Boko Haram ds ba su ma da sanin matakin aikin, amma sai sojojin Najeriya sai su jefar da bindigoginsu, su ruga a guje.
Sojojin suna fada wa mutane cewa daidai da hakkinsu na aiki ba a ba su, to yaya za a yi soja ya yi aiki? To amma wannan lokacin ya canza, ko a talabijin aka nuna, sojoji yanzu a jihohin Barno da Yobe da Adamawa da sauransu, yanayinsu ya canja, fuskarsu suna jin dadin aiki. Don haka an riga an ba su dama, sannan an ba su adadin lokacin da za su gama wannan aikin, kuma in sha Allahu za su yi nasara.