✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba da yawunmu majalisa ta amince da kara wa’adin dokar ta-baci ba – Alhassan Ado

Alhaji Alhassan Ado Doguwa, dan Majalisar Tarayya ne daga mazabar Doguwa da Tudun Wada a Jihar Kano kuma Shugaban Kwamitin Muradun karni (MDGs) na majalisar,…

 Alhaji Alhassan Ado DoguwaAlhaji Alhassan Ado Doguwa, dan Majalisar Tarayya ne daga mazabar Doguwa da Tudun Wada a Jihar Kano kuma Shugaban Kwamitin Muradun karni (MDGs) na majalisar, ya ce ba da yawun ’yan adawa majalisar ta amince da kara wa’adin dokar ta-baci a jihohin Barno da Yobe da Adamawa ba:

Daga Husaini Isah, Jos
Aminiya: A makon jiya ne Majalisar Wakilai ta amince Shugaban Goodluck Jonathan ya kara wa’adin wata shida na dokar ta-baci a jihohin Barno da Yobe da Adamawa duk da cewa al’ummomin jihohin ba sa son a kara wa’adin, me ya sanya majalisar ta amince da wannan lamari?
Alhassan Ado: Ba wai majalisar wakilai baki daya ce ta amince da a kara tsawon wa’adin wannan dokar ta-baci ba. Mu da muke ’yan hamayya a wannan majalisa a karkashin Jam’iyyar APC ba mu yarda a kara wa’adin dokar ta-baci ba, domin ya saba da abin da mutanen jihohi suke nema. Amma tunda majalisa ce da take karkashin shugabanci da jagoranci irin na Jam’iyyar PDP da a kowane lokaci suna karbar umarni ne daga sama kan daidai ko ba daidai ba, saboda haka suka samu damar da aka yi zama a wannan majalisa.  Domin ita majalisa da zarar ta yi zama wadanda suke cikin majalisar a lokacin wannan zama, su ne suke da ikon yin komai. Kuma idan kana wannan majalisa ko ba ka nan duk abin da majalisar ta zartar za a ce kana da hannu a kai. Don haka suka samu suka saci wani lokaci wanda suka fahimci cewa mafiya yawan ’yan majalisar ’yan adawa ba sa nan a majalisar. Musamman a lokacin da ake zabubbukan shugabanin Jam’iyyar APC na jihohi. Yawancin ’yan adawa ba sa nan a lokacin, saboda haka suka samu wannan dama saboda mafi yawansu ’yan PDP ne suka ba Shugaban kasa wannan dama. Yin wannan abu a wurina ya dada tabbatar wa ‘yan Najeriya ne cewa Gwamnatin Tarayya ta kasa. Domin a yau a ce an sanya dokar ta-baci, an kara an sake karawa wannan ya nuna wa duniya cewa gwamnatin Jam’iyyar PDP karkashin Shugaba Goodluck Jonathan ta gaza ba za ta iya ba. Tunda ga shi an wayi gari rashin zaman lafiya a jihohi uku an kasa magance shi, kuma abu ne wanda cikin sauki za a iya warware shi. Saukin shi ne tunda akwai masu da’awar cewa an zalunce su akwai masu da’awar cewa an cutar da su, akwai masu da’awar cewa an kashe rayukansu ba bisa ka’ida ba. Mene ne laifi idan an zauna da wadannan mutane? Mene ne laifi idan an yi sulhu da wadannan mutane? Shawarata idan da gwamnati za ta karya gwiwa ta nemi zaman lafiya da wadannan mutane don a zauna lafiya ba ta fadi ba. Kuma irin wannan fitina ba a Arewa aka fara ba. An samu irin wannan fitina a yankin Neja-Delta, suka tada bama-bamai suka hana hakar mai a yankin. Amma karkashin jagorancin marigayi Shugaba Umaru Musa ‘Yar’aduwa da ya ga maganar bude wuta ba za ta taimake mu ba, ya ce a kirawo wadannan ’yan tawaye a yi sulhu, suka zo aka yi sulhu aka yi masu afuwa aka rika diban kudin Najeriya ana ba su ana kai su makarantu ana horar da su ana ba su kudi suna yin sana’a, aka samu zaman lafiya a yankin.
Kuma wannan Shugaban da ya zo tunda mutanensa ne yankinsa ne ya dada ci gaba da bin wannan tsari na marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa tare da nuna son zuciya da gayya. Yanzu a wannan yanki na Neja-Delta sai ka ga mutumin da bai fi a taimake shi da jarin Naira dubu 50 ko Naira dubu 100 ba. Sai ka ga an ba shi Naira miliyan 50 ko miliyan 100 kuma duk kudaden kasa ne ake amfani da su wajen bin wannan tsari, wannan ba karamin zalunci ba ne. Saboda haka ni ina kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da irin wancan tsari na yin afuwa ga ‘yan Boko Haram. Ba na goyon bayan mutane su dauki doka a hannunsu amma ina goyon bayan mutumin da ya yi kuka ya ce an zalunce shi, kuma ya ce ya yarda a zo a yi sulhu to a yi sulhun da shi. Domin a dakatar da zubar da jinin wadanda ba su ji ba ba su gani ba.
Aminiya: Mene ne ra’ayinka game da gayyato sojojin Amurka da Ingila da Faransa don kubutar da ’yan mata, ’yan makaranta da aka sace a Chibok?
Alhassan Ado: Duk ra’ayina guda ne kan wannan al’amari da kara lokacin dokar ta-baci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa da gayyato sojojin kasashen waje don su magance mana matsalarmu duk sun nuna kasawar Gwamnatin Tarayya ne. Gwamnatin Tarayya karkashin Shugaba Goodluck Jonathan ta kasa. Maganar tabbatar da zaman lafiya a kasa, hidima ce da ta shafi gwamnatin kasa da mutanen kasa.
Kuma ko’ina a duniya ana irin wadannan rigingimu kuma salonsu da tsarinsu yana bambanta. Idan ka dauko Bature ka ce ya zo ya yi maganin irin wadannan rigingimu ta ina zai fara? Yau she ya san abin da yahaddasa irin wadannan rigingimu? Abu ne da muna da maganinsa a gida amma mun fita neman magani a waje. Gwamnati ta dawo ta dubi me ya haddasa wannan rigima, domin ta yi maganin abin. Domin zuwan Baturen Amurka ko Baturen Ingila ko Baturen Faransa wadanda al’adunmu da addininmu ya yi daban da nasu ya shigo ya ce shi ne zai yi mana maganin matsalarmu wannan wasa da hankalin mutanen Najeriya ne. Tuni jama’a sun gano cewa kara wa’adin dokar ta-bacin nan da gayyato Turawa cikin kasar nan, wani kokari ne na a tabbatar an kasa samun rashin zaman lafiya ta yadda in lokacin zaben badi ya zo, a ce ba za a yi zabe ba a wasu sassan kasar nan. Domin a gurgunta jam’iyyar da ake ganin za ta yi nasara a wannan bangare.
Aminiya: Wasu ’yan Najeriya suna zargin ku ’yan majalisun tarayya ba ku tsayawa ku yi aikinku yadda ya kamata don haka ake ta samun wadannan matsaloli?
Alhassan Ado: Ba za ka hana dan Najeriya ya fadi ra’ayinsa kan ’yan majalisun Najeriya ba. Don haka ba na ganin laifin masu fadin ra’ayinsu kan ’yan majalisa. Amma ya kamata mutane su san cewa ’yan majalisa suna suka tara. Domin duk lokacin da aka ce an taru a majalisa muryar mutum daya ba ita ce majalisa ba, idan aka kawo wani abu ko kana so ko ba ka so, idan aka dauki wani matsayi dole ne ka bi. Amma majalisa tana bakin kokarinta wajen yin ayyukanta na farilla, ayyukan majalisa na farilla su ne duba tsarin kasafi. Muna yi a kowanne lokaci kuma ba ma ba gwamnati abin da take so, sai abin da muka fahimci shi ne jama’ar kasa suke so. Aikin majalisa na biyu shi ne wakiltar mutanen Najeriya, kowane dan majalisa ya san yana wakiltar al’ummar mazabarsa ne. Muna tsayawa tsayin daka mu wakilci abin da jama’ar da muke wakilta suke so. daya daga cikin dalilan da suka sa muka fita daga cikin Jam’iyyar PDP ke nan, domin mun lura cewa mutanenmu da muke wakilta daga Arewa sun kosa da Jam’iyyar PDP saboda zaluncinta, don haka muka fita, wannan ya nuna cewa mun bi ra’ayin mutanenmu. Bayan haka aikin majalisa na uku shi ne mu sanya ido kan ayyukan da gwamnati take yi, bayan ta yi kasafin kudi kuma muna sanya ido. Idan aka yi kasafin kudi muna bi ma’aikatu da jihohin Najeriya, domin mu duba mu ga ina ne ba a yi amfani da kudin da aka ware masu ba kamar yadda ya dace. Ina ne aka yi amfani da kudin da aka ware masu kamar yadda ya dace, wadannan su ne ayyukanmu na farilla. Sai dai in ta baci Shugaban kasa ya yi wata ta’asa wanda tsarin mulki ya ba da dama a tsige shi, har zuwa yanzu babu wani abu mai karfi da Shugaban kasa ya yi da za mu iya tayar da kayar baya mu ce a tsige shi ba. Kuma musamman yanayin da muke ciki a kasar nan na rashin zaman lafiya, idan ya zamana mun zo mun hura wutar da za ta rikita gwamnati ina ganin ba mu taimaki kasar ba. Yanayin da muke ciki a kasar nan a halin yanzu na larura ya kamata mu yi hakuri mu dauke kai. Domin muna ganin ya kamata gwamnati ta fuskanci wannan abin a yi maganinsa. Amma daga lokacin da ka shiga rikici da gwamnati a lokacin da kasa take cikin larura ka ga akwai matsala. Wannan shi ne abin da muke fuskanta, kuma shi ne muke kokari mu kiyaye amma ake ganin kamar gazawa ce. Ba gazawa ne muke yi ba, muna kau da kai ne domin muna ganin yanayin da kasa take ciki na rashin zaman lafiya ba shi ne yanayin da za mu hura wa gwamnati wuta ba, a wayi gari a ce mu ne muka ruda gwamnatin ta kasa yin abin da ya kamata ta yi.
Aminiya: To, ina mafita kan wannan al’amari?
Alhassan Ado: Mafita ita ce mu dogara ga Allah tunda dukkanmu masu addini ne. Kowa ya roki Allah ya yi mana maganin wannan hali da muka shiga a Najeriya. Ita kuma gwamnati ta kara jajircewa ta fitar da son zuciya ta yi aikin da ya kamata ta yi.