✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bai wa ƙananan hukumomi ’yanci tamkar an bar baya da ƙura ce — Ngordi

Gwamnoni sun san yadda suke shake wuyan kananan hukumomin, ta hanyar hamdame kuɗaɗensu.

Tsohon Shugaban tsohuwar Jam’iyyar APP a Jihar Yobe, Alhaji Muhammad Ngordi ya ce, bai wa kananan hukumomi ’yancin cin gashin kai tamkar an yi baya ba zani ne domin kuwa har yanzu tsugune ba ta kare ba ga kananan hukumomi da gwamnatocin jihohi.

Alhaji Muhammad Ngordi ne yana bayyana ra’ayinsa ne, a kan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke na bai wa kananan hukumomi ’yancin cin gashin kai.

Ngordi ya ce, matukar ba a yi dokar da za ta bai wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) damar gudanar da zaɓen kananan hukumomi ba, to da sauran rina a kaba, domin idan hukumomin zaɓe na jihohi ne za su ci gaba da gudanar da zaɓuɓɓukan kananan hukumomin, sai wanda gwamnan jiha ke so ne zai iya zama shugaban karamar hukuma a kuma jam’iyyar da take mulkin jihar.

A cewarsa duk abin da gwamna ke so shi ne shugabannin kananan hukumomin jiharsa za su yi, domin in an ce kuɗinsu na wata-wata ya shigo asusun karamar hukuma, to, in gwamna ya ce kada shugaban karamar hukumar ya taɓa ko sisi sai an ba shi umarni, to dole ne ya yi hakan domin gwamnan ne ya zaɓo shi.

Ya ce matukar ba a kakkaɓe hannun gwamnoni daga cikin al’amuran kananan hukumomi ba, to an yi baya ba zani domin lura da tsarin mulki ya ba gwamnonin karfi da iko mai yawan gaske, duk yadda za a yi dole ne sai shugabannin kananan hukumomin sun yi musu biyayya.

“To amma idan kananan hukumomi suka koma hannun wata hukuma da za ta kula da su daga Gwamnatin Tarayya kuma aka gudanar da zaɓen kananan hukumomin cikin ’yanci a karkashin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yadda za a samu wasu jama’iyyun adawa sun ci wasu kujeru a jihohin da ba jam’iyyarsu ne ke mulkin ba, to kuwa akwai tabbacin a samar wa kananan hukumomi ’yanci mai ma’ana,” in ji shi.

Alhaji Muhammad Ngordi ya kara da cewa, “In Gwamnatin Tarayya ta yi sako-sako da wannan lamari to zai kasance tamkar an kashe maciji ne, ba a sare kansa ba domin babu abin da zai sake a ɓangaren kananan hukumomi.

“Game da wa’adin da ake zargin gwamnoni sun nema na a kara wata uku, kafin a fara bai wa kananan hukumomi kuɗaɗensu kai-tsaye, hakan ya tabbatar da cewa gwamnonin sun san yadda suke shake wuyan kananan hukumomin, ta hanyar hamdame kuɗaɗensu, maimakon a kyale su, su yi wa al’umma ayyukan raya kasa.

“Sannan gwamnonin sun yi haka ne domin su samu damar gudanar da zaɓuɓɓukan kananan hukumomi ta hanyar zaɓo shugabannin da za su kasance masu yi musu biyayya,” in ji shi.