✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba da tazarar haihuwa Musulunci ya amince a yi ba kayyade iyali ba — Jabir Maihula

An shirya taron ne don tattaunawa batutuwan guda biyu

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke jihar Sakkwato, Dokta Jabir Sani Maihula ya bayyana yadda addinin ya amince da ba da tazarar haihuwa amma bai yarda da kayyade iyali ba.

Malamin ya bayyana hakan a wurin taron yini daya da kungiyar Breakhrough Action ta gudanar a dakin taro na Dan Kani a Sakkwato a wannan Laraba.

A cikin wata makala da ya gabatar mai taken ‘Gudunmawar mazaje a wurin samar da tazarar haihuwa’, ya ce addinin ya fayyace komai a kan batutuwan biyu.

Malamin ya ce, “Bayar da tazarar haihuwa na nufin samar da tsari a tsakanin yaran da za a haifa domin sha’anin kiyon lafiya da samar da sauki ga mahaifiyar yara a wurin reno.

“Kayyade iyali kuwa saboda tsoron talauci kuskure ne addini bai aminta da hakan ba, ba inda aka ce mutum ya haifi yawan kaza ya tsaya.”

Dokta Jabir ya kuma ce inda kalubalen yake a tsakanin abubuwan guda biyu shi ne yadda za a fahimtar da gama-garin jama’a domin su malamai da sauran jagorori sun fahimta, abu ne da za a samar da tsari da za a tafi tare da kowa.

Da take nata jawabin, Uwargidan Gwamnan jihar Sakkwato, Mariya Aminu Waziri Tambuwal ta ce ta saba halartar irin wannan taron domin muhimmancinsa a gare ta.

Ta kuma ce ta hada kai da kungiyoyi suna aiki tare domin kawar da cin zarafin mata a cikin al’umma.

Mariya, a ta bakin wakiliyarta, Fatima Khalid, ta ce tana alfahari da wannan taron na hada malaman addini da sarakunan gargajiya wuri daya domin samar da mafita a kawar da cin zarafin mata.

Shi kuwa Shugaban kungiyar ta Breakhrough Action a Sakkwato, Dokta Abdurrahman Zagga ya ce makasudin shirya taron shi ne domin malamai da sarakunan gargajiya a fadin jihar su hadu su tattauna batutuwan guda biyu.

“Muna so mu duba gudunmuwar mazaje a wurin tazarar haihuwa, matsayin mata a wurin zartar da hukunci, mu’amalar ma’aurata a wurin kare cin zarafin jinsi a mahangar addini da al’ada da sauransu,” inji shi.