Amma Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa,‘Ba da gurasa kaxai mutum zai rayu ba,
Sai dai da kowace maganar da take fitowa daga wurin Allah.’” (Matiyu 4:4)
Muna yi wa Ubangiji godiya domin qaunarSa mara iyaka. Za mu c igaba da nazari a kan ikon da cikin Kalma/Maganar Ubangiji.
Bari mu duba Littafin Ishaya 55:8-11, Ubangiji Ya ce, “TunaniNa ba kamar irin naku ba ne. Al’amuraNa kuma daban suke da naku. Kamar yadda sammai suke can nesa da qasa, Haka al’amuraNa da tunaniNa suke nesa da naku. MaganaTa kamar dusar qanqara take. Kamar kuma ruwan sama da yake saukowa domin ya jiqe duniya. Ba za su kasa sa amfanin gona ya yi girma ba. Sukan ba da iri domin shukawa, da abinci kuma domin a ci. To, haka maganar da Na faxa take. Ba ta kasa cika abin da Na shirya mata. Za ta yi kowane abin da Na aike ta ta yi.”
Idan muka duba baya lokacin da Ubangiji Ya yi halitta, cikin Littafin Farawa, za mu ga cewa kalmarSa kaxai ta sa sammai da abubuwan da ke cikinta, qasa, teku da halittu da ke cikinta suka bayyana. Ba wai ba, ba za mu iya haxa tunanin Ubangiji da namu ba, gama Ya ce tunananiSa ba kamar irin namu yake ba, hakan nan kuma al’amuranSa na nesa da namu. Shi ya sa ya kamata mu ba da gaskiya ga ikon da maganar Ubangiji ke xauke da shi, mu ci moriyar wannan zarafi. Mu bar dogara ga abin da muka mallaka, mu bar dagara ga ikon tunaninmu ko tattalinmu, bari Kalmar Ubangiji ta zama abu na farko cikin tunaninmu a koyaushe, muna kuma dogara ga ita, ta wurin haka ne za mu rayu.
Shin, mene ne rayuwa? Rayuwa ba ita ce abubuwan da muka mallaka ba, kamar yadda waxansu da dama ke tunani, za ka ji suna cewa ai na gaji gidaje ko mu ce dukiya mai ximbin yawa, ina da gidaje da motoci da dama a duk faxin duniya da kuxaxe a ko’ina cikin bankuna, zan iya cin duk irin abincin da na ga dama in za ga ko’ina a duk faxin duniya, in kuma sa ’yan agaji su kare ni da dukan iyalaina. Kash, wannan ita ce wautar da Ubangiji ke nufi, wadda Yesu ya ba da misali da mai arzikin da muka karanta a makon jiya. Duk abubuwan nan da muka ambata ba sa ba da rai, idan kuma muka duba, za mu ga cewa rai shi ne abu mafi muhimmanci cikin rayuwar xan Adam, shi ya sa ba za mu tava samun rai ko rayuwa cikin arzikinmu ba, sai dai cikin maganar da take fitowa daga wurin Ubangiji Allah kaxai. Ubangiji Allah Shi Ya yi komai, Shi ne kuma Mai komai da kowa, Yana matuqar qaunarmu shi ya sa ya halicce mu cikin rayayyu, bai kuwa nemi shawarar kowa ba, lokacin halittarmu, lokacin da Ya halicce mu kuma bai dunqula kuxi ko gidaje cikin wani qunshi Ya ce ga shi, ka je ka rayu ba, abin da ya fi muhimmanci ne Ya ba mu; wato rai, Ya busa mana numfashin rai domin mu rayu. Ya ce zai tanada mana duk abubuwan da muke buqata na rayuwa wato buqatunmu na yau da kullum. Ta kowane vangare tun daga farkon halittar duniya Ubangiji na da iko bisa komai, shi ya sa Ya ce bari dogararmu ta kasance bisa kalmarSa kaxai amma ba abubuwan da muka mallaka ba, domin komai da kowa mai shuxewa ne amma maganar Ubangiji Allah za ta kasance har abada. Abu na farko mafi muhimmanci shi mu zama da sanin cewa Ubangiji Allah ba mutum ba ne da zai yi qarya. Littafin Qidaya: 25:19: Allah ba kamar mutum ba ne da zai yi qarya. Ba kuwa xan mutum ba ne da zai tuba. Zai cika dukan abin da Ya alqawarta. Ya furta, ya kuwa cika.”
Ishaya 40:8: “Haqiqa ciyawa takan bushe, furanni kuwa su yi yaushi. Amma maganar Allah ba za ta taɓa faxuwa ba!”
Domin haka sai mu sabunta tunaninmu cikin rayuwa, mu zama masu iko cikin sabon hali na dogara ga ikon rayuwa cikin maganar Ubangiji. 1 Bitrus 1:23: “Gama sake haihuwarku aka yi, ba ta iri mai lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, wato, ta Maganar Allah rayayyiya dauwamammiya. Domin “Duk xan Adam kamar ciyawa yake. Duk darajarsa kamar furen ciyawa take. Ciyawar takan bushe, furen yakan kaxe, Maganar Ubangiji kuwa dauwamammiya ce.” Ita ce maganar bishara da aka yi muku.”
Zabura 119: 89: “MaganarKa tabbatacciya ce, ya Ubangiji. A kafe take a sama. Amincinka ya tabbata har abada. Ka kafa duniya a inda take, tana nan kuwa a wurin. Dukan abubuwa suna nan har wa yau saboda umarninKa, Domin su duka bayinKa ne. Da ba domin dokarKa ita ce sanadin farin cikina ba. Da na mutu saboda hukuncin da na sha. Faufau ba zan raina qa’idojinKa ba. Gama saboda su Ka bar ni da rai. Ni naKa ne, Ka cece ni! Na yi qoqari in yi biyayya ga umarninKa. Mugaye suna jira su kashe ni. Amma zan yi ta tunani a kan dokokinka. Na koyi, cewa ba wani abu da yake cikakke. Amma umarninKa ba ya da iyaka.”
Bari Ubangiji Allah Ya ba mu gane ikon rayuwa da ke cikin maganarSa, amin.