Ahmad Babba Kaita shi ne Sanata mai wakiltar Arewacin Katsina a Majalisar Dattijai, yankin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fito.
A wannan tattaunawa da Aminiya, Kaita ya yi bayani dangane da Sashi na 84(12) na Dokar Zabe da matsalolin da Jam’iyyar APC ke fuskanta da tsarin karba-karba da kudurinsa a 2023 da kuma yanayin da Jihar Katsina take ciki a yanzu:
Tun bayan da wata Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci game da Sashi na 84(12) na Dokar Zabe ta 2022, rudani ya baibaye al’amarin. Me za ka ce game da wannan al’amari?
Bari in fara da bayyana maku cewa, hatta yanayin da aka shigar da kara game da al’amarin a Umu’ahiya ya kasance abin zargi da ban dariya.
Hedikwatar Hukumar Shari’a da Majalisar Dokoki ta Kasa duk suna Abuja, amma duk da haka sai aka tafi Umu’ahiya aka shigar da kara.
Wannan shi ne abin dariya daga al’amarin shari’ar nan kuma mun san cewa mai shari’ar yana da alaka da ofishin Antoni Janar na Tarayya. Haka kuma na yi amanna cewa an shigar da wannan kara ce da nufin samar wa wadansu da suke son takara lokaci. In sha Allahu ba za mu bar abin ya yi nasara ba.
Me kake zaton ya sa ofishin Antoni Janar ya yi gaggawar killace wannan hukunci kuma aka fara amfani da shi?
Ai al’ummar kasar nan tuni suka yi amanna da cewa wadansu hamshakai ne a gwamnati a Bangaren Zartarwa suka kulla wannan al’amari na kalubalantar wannan doka a kotu.
Ni dai ban taba ganin inda kotu ta soke dokar da Majalisar Dokoki ta Kasa ta samar ba, bayan Shugaban Kasa ya sanya mata hannu.
Babu wata kotu da take da wannan ikon kuma idan har kotu ta yi haka, to ke nan ashe kowane bangare na gwamnati bai da ikon cin gashin kansa.
Abin da kawai kotu ke da ikon yi shi ne ta tantance ko wannan doka ta yi karo da wata, ta bayar da shawara majalisa ta gyara, amma ba ta da ikon soke ta gaba daya.
Akwai wata doka a kundin tsarin mulkin 1999 da ta ce duk wani ma’aikacin gwamnati da ke son yin takarar siyasa, dole ya ajiye aiki wata daya kafin shiga zabe amma wannan doka ta yanzu ba a kan ma’aikatan gwamnati take magana ba, tana magana ne a kan masu rike da mukaman siyasa, wadanda ba zabensu aka yi ba.
Kuma mun samar da wannan doka ce da nufin tsarkake dimokuradiyya. Idan aka bar tsarin haka sakaka, masu rike da mukaman siyasa za su iya amfani da dukiyar gwamnati wajen biyan bukatunsu na siyasa, wanda hakan ba daidai ba ne.
Abin da muke bukata shi ne, dukkan wadanda suke son takara daga cikin masu rike da irin wadannan mukamai, su ajiye mukamansu tukunna, kwana 180 kafin zabe, su tuntubi masu zabe su nuna masu cancantarsu, domin su zabe su, ba kawai su yi karfa-karfa ba, ta amfani da mukamin gwamnati da dukiyarta.
Ba ka tunanin ko Shugaban Kasa na goyon gayan soke wannan batu da ke cikin dokar, musamman ganin yadda yarubuta wa majalisa takarda don bukatar haka?
Ina da masaniyar cewa duk abin da Shugaban Kasa zai yi, yana yin sa ne da kyakkyawar niyyar kyautata wa al’ummar Najeriya, ba ni da kokwanto a kan wannan.
Wata matsala a nan ita ce, a lokacin da wadansu mutane da suke kewaye da shi suke da wata bukata ta kashin kansu, za su yi iya kokarinsu don ganin sun ja ra’ayinsa ya yi abin da suke so, wanda zai amfane su. Wannan ba wani boyayyen al’amari ba ne a duk duniya, Shugaban Kasa dole ne ya nemi shawarar mutanen da ke tare da shi kuma lallai akwai yiwuwar su rinjaye shi da shawarar da za ta amfane su a siyasance.
Babu shakka mun san Shugaban Kasa yana da niyya mai kyau amma a wannan batu, mai ba shi shawara ta fuskar shari’a shi ne Antoni Janar kuma kowa ya san yana da niyyar yin takarar Gwamna a jiharsa ta Kebbi, domin fostarsa ta cika ko’ina a jihar.
Kuma kada mu manta da cewa, shi kansa Shugaban Kasa mutum ne da ya goyi bayan a baje takara kowa ya fafata, kato-bayan-kato.
Wannan tsarin ne ma ya ba shi nasara a baya, musamman lokacin da ya ankara cewa attajiran ’yan takara da ke takama da tarin kudi za su iya kawo masa cikas.
Amma a yanzu ina ganin kamar na kusa da shi sun ba shi gurguwar shawara ce dangane da al’amarin saboda biyan bukatunsu.
Kuma a lokacin da dan takara ke tsoron a fafata takara a dimokuradiyance tun daga cikin jam’iyya, ta yaya zai iya yin takara da jam’iyyar adawa a babban fagen zabe?
Ke nan za ka shawarci majalisa ta daukaka kara dangane da wannan hukunci na kotun?
Babu shakka wannan al’amari da ya faru tamkar raini ne ga majalisa a matsayinta na daya daga turakun gwamnati, don haka shugabannin majalisa na da hakkin kare martaba da mutuncinta.
Suna da ikon shirya daukar matakin da ya dace na dakile wannan hukunci na kotu.
Koda shugabannin majalisa ba su dauki irin wannan mataki ba, tuni wasunmu da ke da muradi kan batun muka fara tuntubar lauyoyinmu domin daukaka kara.
Ni dai ban taba ganin inda dokar da majalisa ta samar kuma ta cika dukkan ka’idoji, sannan Shugaban Kasa ya rattaba mata hannu, amma a ce wata kotu ta soke ta ba.
Wannan ne karon farko da na taba ganin haka kuma lallai abin ba zai zauna haka ba, sai an dakile shi.
Ga shi jam’iyyarku ta APC ta mika wa Arewa mukamin Shugaban Jam’iyya ta Kasa, shin wannan yana nuni ne da cewa wanda zai gaji Buhari a matsayin Shugaban Kasa zai fito ne daga Kudu?
Na sha fadin cewa ni mutum ne da ya yi amanna da yarjejeniya a siyasa.
Duk yadda kake da wani korafi ko kaikayi game da yankin Kudu maso Yamma, tabbatacciyar magana ita ce yankin ya taimaka mana muka samu nasarar zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Don haka adalci ya gaya mana cewa abin da Bala ke so to shi ma Bulus yana so.
Na yi amanna cewa yankin Kudu ya kamata ya samar da Shugaban Kasa a wannan karo, domin mun cinye shekararmu takwas.
Ya kamata a yi masu adalci su ma su fitar a wannan karon, domin samar da hadin kan kasa da daidaito.
Wane yanki na Kudu kake ganin ya kamata ya samar daShugaban Kasa a jam’iyyar taku?
A takarar siyasa irin wannan, a duk lokacin da aka ce an amince wa yanki kaza ya fitar da Shugaban Kasa, ya rage ruwan yankin ya yanke hukuncin bangaren da suka amince ko Yamma ko Kudu.
Haka abin ya faru a lokacin da aka ba Arewa dama, an bar mana wuka da nama, muka zabi wanda ya samu nasara.
Kuma lallai ne a sanya hikima da basira a batun. Idan aka ce dole sai kowane yanki ko kuma kowace jiha sai ta samar da Shugaban Kasa, za mu haifar da babbar matsala.
Don haka a kyale al’ummar yankin su yanke wa kansu hukuncin wanda suke so.
Mece ce matsayarka game da Jam’iyyar APC a jiharka ta Katsina?
Batun gaskiya a Jihar Katsina ba mu farin ciki, domin kuwa abin da ke faruwa ba shi al’umma suka zata ba, musamman idan aka yi la’akari da irin goyon baya da kaunar da al’umma suka nuna mana a lokacin da mulki ya zo hannunmu.
A Jihar Katsina, babu abin da ake shukawa sai lalata dukiyar gwamnati.
Idan na ce zan zayyana abubuwan takaicin da ke faruwa a Katsina, zan yi haka ne ina zubar da hawaye. Domin kuwa Gwamnatin Masari ba kawai ta lalata shekara takwas ba ce kadai, a’a, ta maida mu baya na tsawon wata shekara takwas ce.
A halin da ake ciki gwamnatin ta tsiyace. Babu wasu gine-gine ko ayyukan raya kasa kuma ilimi da muka yi alkawarin bunkasawa, ya tabarbare.
A tarihin jihar, wannan ne yanayi mafi muni dangane da tabarbarewar harkokin ilimi. Haka al’amuran suke a sauran sassan rayuwa da ma’aikatun gwamnati.
Mu dai a Jihar Katsina, a bangaren shugabanci, babu abin da ke akwai sai takaici. Ga duk mai son tabbatarwa, zai iya bincikawa, babu abin da yake a boye.
Ta yaya kake ganin wannan yanayi zai shafi nasarar jam’iyyar a jihar a badi?
A yadda ake ciki, har yanzu dai ina cikin Jam’iyyar APC amma ina tabbatar maka cewa a yadda al’amuran siyasa suka dumama a Katsina a yau, nasarar jam’iyyar kamar a ce rakumi ya wuce ta cikin allura ne, domin kuwa tun shekara bakwai da ta gabatar, gwamnatin jihar ta watsar da al’umma.
Daidai da zaben kananan hukumomi, gwamnatin ta kasa gudanarwa har zuwa yau. Wannan abin takaici ne matuka. Amma a halin yanzu muna ta kokarin mu ga mun samar da jajirtaccen gwamna wanda ya san abin da ya kamata.
Kullum ina ba da misali da Gwamna Zulum da El-Rufa’i, cewa su ne gwarazana, domin a koyashe a tsaye suke suna aikin da ya dace amma sauran jihohi, har da Katsina sai takaici kawai.
Ana sa ran za a gudanar da zabubbukan fitar da gwanaye tsakanin watan Afirilu zuwa Yuni, wane mukami za ka yi takara?
Har yanzu dai ni Sanata ne mai ci, don haka bari mu ketare gadar tukunna. Zuwa yanzu ina kan tuntubar dimbin al’ummata da kungiyoyi a Katsina, har da sarakuna da dattawa.
Kuma yanzu ba batun takara ke da muhimmanci a gabana ba. Abin da ke gabana shi ne in tabbatar da cewa na yi abin kirki ga al’ummata, ya rage ga mutane su duba abin da na yi masu, idan sun yaba, to, na gamsu.
Na yi iya kokarina wajen yin ayyuka ga al’umma a jihata. Nakan gane haka ne ta yadda mutane ke murna da ni a ko’ina a Jihar Katsina. Wannan shi ne abu mafi muhimmanci a gare ni fiye da wata kujerar siyasa.
Kullum ina fadin cewa damuwata ta Jihar Katsina ce gaba daya.
Mukan ga yadda kake yawan wallafawa a shafinka na Facebook, kana kiran mutanen mazabarka su zo su amshi takardun guraben aiki da ka sama masu. Ta yaya kake samun nasara a wannan fage, abin ko wani siddabaru ne?
Babu wani siddaru a wannan batu. Na yi amanna cewa babban abin da mutum zai yi shi ne ya gina al’umma, ya kafa tarihin abin alheri a lokacin da ya samu dama.
Muna da babbar matsala a Arewa, musamman yadda matasa da yawa, wadanda suka kammala jami’a amma babu aikin yi. Idan ba mu gina su ba, mun rasa su ke nan a rayuwa, domin a duk lokacin da mutum ya rasa alkiblar rayuwa, kamar ya mutu ne.
Na samar da wani sashi a karkashin ofishina, wanda aikinsa shi ne ya rika binciko duk inda ake da guraben aiki a kasar nan. Nakan je irin wadannan ma’aikatu da kaina in zauna na tsawon lokaci a matsayina na Sanata, ina jiran shugaban ma’aikatar domin ganawa da shi. Nakan daure har sai na samu gurbi daya ko biyu domin matasanmu.
Aiki ne mai wuya da cin rai, wani lokaci ma har da kaskanci amma hakan nake yi cikin dauriya.
A karshe ga irin nasarar da nake samu. Babu shakka ina farin ciki da yadda nake faranta wa yaranmu ta hanyar sama masu ayyukan yi.
Zuwa yanzu ko za ka iya gaya mana adadin mutanen da ka samar wa aiki?
A kashin gaskiya ba zan iya sanin yawansu ba. Alhamdulillahi!