✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a yi wa zawarawa adalci

Dole na jinjina wa gwamnatin Kano da ta fito fili ta nuna wa zawarawa kauna kuma ta yi musu gata ta hanyar aurar da su…

Zawarawan da Gwamnatin Jihar Kano ta aurar a kwanakin bayaDole na jinjina wa gwamnatin Kano da ta fito fili ta nuna wa zawarawa kauna kuma ta yi musu gata ta hanyar aurar da su ga mazajen da suke kauna ta hanyar hukumar Hisba ta jihar. Hakazalika ba zan manta da mata wadanda suka kafa kungiyoyin kare ’yancin zawarawa ba a jihohinmu. To amma duk da haka har yanzu zawarawa na cikin halin ni-’ya-su saboda kyama da kuma wulakancin da ake yi musu.
Zawarawa a yanzu sun zama saniyar-ware a cikin al’umma ba don komai ba sai don rashin tsari da muke da shi a Arewa. Mafi yawan maza a yanzu babu abin da suke yi da zawarawa sai mayar da su gugar-yasa da sun gama amfani da su sai su yi watsi da su.
A yanzu idan mace aurenta ya mutu ta dawo gida sai ka ga ta zama abar kwatance a tsakanin al’umma da ’yan uwa da kuma kawaye. Maimakon a tallafa mata sai a kyale ta da matsalolinta, babu wanda ya damu da ita. Idan ta yi rashin sa’a iyayenta ba su da abin duniya to ta shiga-uku, domin samun kudin  kashewa da na abincin da za ta sa a bakin-salati zai rika yi mata wahala. Saboda haka sai ka ga ta shiga tasku. Idan kuwa ta yi sa’a iyayenta masu rufin asiri ne ko masu hannu da shuni sai ka ga ana rubibinta, maza na yi mata layi ba don komai ba sai don abin da za su samu tare da ita. Wadansu ma har kokari suke yi su aure ta don kawai su samu abin duniya ko kuma su samu alfarma idan daga gidan sarauta ko mulki ta fito.
Gaskiya ya kamata zawarawa su farka daga barcin da suke yi su san cewa don mace aurenta ya mutu ba shi ne karshen rayuwarta ba. Kada ta bari mutuwar aure ta dakushe ta wajen cim ma burin rayuwarta. Ta yi duk abin da za ta iya ta inganta rayuwarta ta hanyar koyon sana’a da karatu. Idan kuwa ma’aikaciya ce to ta mayar da hankali ga aikinta. Kada ta bari ’yan gulma da tsigwididi su kawar mata da hankali. Idan kuwa tana da ’ya’ya to ta yi kokari wajen ba su tarbiyya mai kyau, kada ta saurari mahaifinsu musamman ma idan yana cikin mazajen nan da ba su damu da yaran da suka rabu da da iyayensu ba.
Ya kamata mu maza mu ji tsoron Allah mu rika hakuri da matanmu. Mu sani su mata suna da rauni kuma mu sani raunin da Allah Ya yi musu karramawa ce gare su. Mu tausaya musu. Idan kuwa Allah ya kaddara rabuwa to mu rabu  da su lafiya. Bayan mun rabu da su kada mu rika cin dunduniyarsu da kyamar su, kada mu yi watsi da su, mu tausaya musu mu tallafa musu.
Ya kamata shugabanni da masu hannu da shuni su rika taimaka wa zawarawa su  kuwa malaman addini ya kamata su rika fadakar da maza muhimmancin auren bazawara da taimaka mata. Su kuwa mata su ji tsoron Allah su rika hakuri da mazajensu. Su sani gidan miji ya fi gidan iyaye komai arzikin da suke da shi Su sani cewa aure shi ne darajar ’ya mace.
Wata matsala da na lura da ita shi ne, mafi yawan zawarawa ba sa son gaskiya kuma ba sa son a fada musu gaskiya. Kun ga haka babbar matsala ce. Ya kamata zawarawa duk lokacin da wani wanda yake son su ya nemi ta fada masa gaskiyar lamarinta to ta ji tsoron Allah ta fadi gaskiya. Su kuwa iyaye bai kamata su rika yin watsi da ’ya’yansu ba don kawai sun zama zawarawa. Su sani da zarar yarinya ta rabu da mijinta babu abin da take bukata sai lallashi da shawara da taimako da kuma addu’a. Allah Ya taimake mu. Abu-Ammar Legas 08027406827