✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a yi wa Rahama Sadau adalci ba – Adam Zango

Fitaccen Jarumi Adam A. Zango ya ce masana’antar finafinai ta Kannywood ba ta yi wa jaruma Rahama Sadau adalci ba saboda dakatarwar da ta yi…

Fitaccen Jarumi Adam A. Zango ya ce masana’antar finafinai ta Kannywood ba ta yi wa jaruma Rahama Sadau adalci ba saboda dakatarwar da ta yi mata a kwanakin baya.

Adam Zango ya yi zargin ne yayin da yake tattaunawa da gidan rediyon BBC a shrinsa na Gane Mini Hanya a karsehn makon da ya gabata.

Ya ce jaruma Rahama Sadau ba ita ta fara yin laifin da masana’antar ta dakatar da ita ba.

“Har yanzu a cikin masana’antar fina-finai akwai wadanda idan suka yi laifin ina tabbatar maka da cewa ba za iya dakatar da su ba”. Inji shi

Ya dage a kan cewa idan da gaskiya ake yi a masana’antar da ba za a samu wadanda suka fi karfin doka ba.

Amma kamar yadda ya ce akwai wasu shafaffu- da- mai wadanda idan ma an dakatar da su bayan kwanaki kadai a dage dakatarwar.

Ya zargi shugabannin kungiyar da nuna kwadayi tare da rokon jarumai kudin abinci.

“Akwai wadanda idan ma an dakatar das u bayan kwana daya ko biyu sai a ce an dage su ci gaba. Ko idan ma kai da kake shugaban wadanda suka yi hukunci watakila wani daga cikinku yana zagayawa gidan jarumai ya ce gidansa babu abinci ta dauki dubu 50 ta bashi”. Inji shi.

Ya ce idan shugabannin suka zama suna rokon na kasa da su babu yadda za su iya hukunta su.

Saboda haka sai ya ce shi ya sa yake girmama na gaba da shi don gudun samun wata matsala.

Ya bayyan cewa a matsayinsa na wanda ya sa mu tarbiyyar daga gida bai taba zagi ko yi wa daya daga shugabbnin Kannywwod rashin kunya.

Jarumin ya dage a kan cewa ba zai bar sana’ar fim ba har zuwa karshen rayuwarsa saboda alfanun da yake cikinta.

Ya bayyana cewa ban da harkar man fetur babu abin da ya fi sana’ar fim samun arziki saboda haka ya ce shi ya sa yake sanya iyalinsa cikin harkar.