Karamin Ministan Tsaro a Najeriya Bello Matawalle, ya caccaki masu sukar lamirin Shugaban Kasa Bola Tinubu game da nuna wariya ga yankin Arewacin Najeriya.
Matawalle ya ce Tinubu kadara ne ga Arewa kuma ba shi da fatan da ya wuce ganin ya magance matsalolin da suka addabi yankin kafin 2027.
Cikin wani jawabi da mai taimaka masa kan sha’anin siyasa Ibrahim Danmaliki Gidan Goga ya fita, Matawalle ya ce ba a taba samun lokacin da ake yin dimokradiyya mai tsafta kamar a zamanin Bola Tinubu ba.
’Yan Najeriya miliyan 150 sun samu ingantacciyar wutar lantarki – Minista
Ya ce duk masu kushe salon mulkinsa kawai suna huce haushin rashi ne da yada farfaganda da karairayi.
“Mutanen Arewa suna da wayewar da sun fi karfin a yaudare su domin cimma wata manufar siyasa. Akwai bukatar mu hada kai waje daya kada mu yarda a yaudare mu.” Inji Matawalle.
Ministan ya ce kamata ya yi a gode ma Tinubu saboda yadda yake inganta yankin Arewa da tsaro kuma ana ganin ci gaba musamman yankin da ya fito na Sokoto-Kebbi-Zamfara.
Bugu da kari ya yaba ma ayyukan ci gaban da yake kawo wa yankin musamman yadda ake shimfida tituna da kokarin kawo ci gaba ga yankin.