✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a ritaya a aikin jarida – Bashir Sama’ila Ahmed

A ci gaba da kawo muku gwagwarmayar fitattun ’yan jaridar da suke raye musamman a wannan shiyya ta Arewa, Aminiya ta tuntutbi fitaccen dan jaridar…

A ci gaba da kawo muku gwagwarmayar fitattun ’yan jaridar da suke raye musamman a wannan shiyya ta Arewa, Aminiya ta tuntutbi fitaccen dan jaridar nan Bashir Sama’ila Ahmed wanda a tallar kamfanin jiragen sama na Kabo ya zare da sunan Malam shi da abokin tallarsa marigayi Usman Yaro da aka fi sani da Manu, domin jin tarihinsa da irin nasarorin da ya samu a aikin jarida da kuma matsalolin da ya fuskanta da shawarwarin da zai ba ’yan baya:

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinka?
Da farko sunana Bashir Sama’ila Ahmed, da nakan ce a haife ni a wani kauye da ake kira Kakangi, to daga baya na tabbatar ba a Kakangi ba ne a Karau-Karau ne a karamar Hukumar Giwa, a lokacin ana karamar Hukumar Zariya ne. An haife ni a 1944, wato shekara daya kafin gama Yakin Duniya na Biyu. A lokacin mahaifina Malam Sama’ila Ahmad yana aikin dubagari a Kudancin Zariya, to daga baya aka yi masa canjin wurin aiki ya dawo Zariya, to ni ma an dawo da ni Zariya, a nan Zariya na tashi na yi karatum Muhammadiyya (addini) da karatun boko, na yi firamaren Kamara a Zariya, kuma na yi babbar firamare a Soba, sannan na dawo Sakandaren Alhudahuda, Zariya. Bayan na kammala sakandare sai aka yi wa su Sardauna juyin mulki. To da zan shiga Jami’ar Bayero ta Kano, a lokacin ana kiranta Kwalejin Bayero, da aka yi juyin mulkin; kasancewar mahaifina yana da mukami a siyasa, to a wannan lokaci sai kawai komai ya koma baya, wato abubuwa suka tsaya, saboda haka ban samu na shiga jami’a ba, sai na dawo na fara aiki da En’e ta Zariya. Daga baya aka zo aka kawashe mu a aikin kwastam daga aikin kwastam da muka shiga dole ba a kan ina so ba, sai na balle na shiga aikin gidan rediyo a 1968. To daga nan na yi ta tafiya har dai na je BBC Landan na yi aiki, kuma na karo karatu, domin su can ba su da tsanani idan kana aiki da su, to za su ba ka damar karo karatu. Na yi aiki a BBC Landan na tsawon lokaci na tafi a Disamba 1974 na dawo watan uku 1978, kuma na tafi ne takanas domin aikin amma na karo ilimi.
Aminiya: To, ka kudirin yin aiki jarida ne tun kana yaro, ko ka tsinci kanka ne kawai a ciki?
Eh, ina da sha’awar aikin jarida, domin ina yaro nakan yi sha’awar irin mutanen da nakan ji muryoyinsu. Saboda haka daga makaranta na fara shiga kungiyoyin muhawara domin in koyi yadda ake ilimantar da kawuna, wato irin wannan kungiyoyin za su kara min fahimtar yadda ake fadin ra’ayi. Ka ga tun daga nan na fara diban aikin jarida, na bar aikin kwastam din da aka sa ni dole na je aikin gidan rediyo.
Aminiya: ka shekara nawa kana aikin jarida?
To idan haka ne har yau ni dan jarida ne, tunda har yau ina yi, amma in ka dauki tun daga 1978 har zuwa yau 2014 ka ga shekara 48 ke nan na yi ina cikin aikin jarida.
Aminiya: Da su wa ka yi aiki a wancan zamani?
To, mun yi aiki da mutane da dama, amma wadanda zan iya tunawa a lokacin da na shiga na tarar da manyan mutane kamar su Alhaji Abba Zuro da James Audu da Madu Mailafiya da Babagana Kingibe da kuma Shetima Wada, wanda ya taba yin Ministan Gona, kai suna da dama da yawa da ba zan iya tuna su ba.
Aminiya: Da Gidan Rediyon Najeriya ka fara aiki ko kuwa?
A nan na fara aiki, amma a lokacin ana kiransa Gidan Rediyon Jihar Arewa, (Broadcasting Company of Northern Nigeria- BCNN), saboda Sardauna ya kafa shi ne domin mutane jihar baki daya. Amma da Gidan Rediyo Jihar Arewa na Rediyo Talabijin Kaduna, su ne masu shi kafin Gwamnatin Tarayya ta zo ta hade su suka zama Gidan Rediyon Tarayya.
Aminiya: A wancan lokacin gidan rediyon yana da shekara nawa ka fara aiki a wajen?
To, na fara aiki da gidan rediyon yana da shekara shida, domin an bude shi ne a 1962, ni kuma na fara aiki da shi a 1968, ka ga shekara shida ke nan da budewa.
Aminiya: Wane kalubale ne ka fuskanta a aikin jarida?
Akwai su da yawa, domin tsarin rayuwarka ne baki daya ya canja, domin daga lokacin da ka shiga aikin jarida a wannan lokaci sai ka ga cewa duk abin da yake naka, to ya tashi daga naka. Ni a kaina wane ne a’a, daga lokacin ya koma na jama’a, domin tsarin rayuwar baki daya zai canja, duk abin da kake fafutika domin ka yi wa kanka, sai ya zama ba naka ba ne na jama’a ne, domin ka fadakar da su ka wayar musu da kai a kan wani abu, to babu canji da zai samu mutum farat daya irin wannan.
Aminiya: Wadanne nasarori ka samu a aikin jarida?
Alhamdullilah, na samu nasarori da dama, domin Allah cikin ikonSa Ya bude aikin jarida gare ni, tunda na yi abubuwa wadanda idan ban don aikin jaridar ba, ban isa in yi ba sai dai idan Allah Ya kaddara maka sai ya same ka, kuma sai ka hadu da shi. Amma ni dai ta sanadin aikin rediyo, na san jama’a, jama’a sun san ni, kuma na san manyan mutane. Dalilinsu duk inda za ka shiga sai an yi maka iso kafin ka shiga, to ni idan na je da wannan sunan zan shiga. Kuma na yi aikin Hajji sau biyu ta aikin rediyo. Aikin jarida ya kai ni kasashen duniya da dama da watakila ina zaune ne ba aikin nake yi ba, ba za ni ba, kuma na yi shirye-shirye wadanda har yau 2014 muna zumunci da su, kamar irin su “Basafce dan Malam Dogara, Na Kumatu Mai Karen Kamun Kura, da irin su Kyaftin Kokodayi da sauransu, kuma wadanda nasarorin da suka jawo suna da yawa kwarai, domin duk dan Adam yana auna wani matsayi na dan Adam dan uwansa. Idan ka ce wani abokinsa makanike ne sai ya raina, amma idan aka ce Basarake ne ko wani babban soja, to ya fi son haka, to ni duk na hada sama da kasa irin wannan.
Aminiya:Ga shi ka ambato shirin Basafce, tun ina dan yaro nake jin shirin kuma shiri ne na mutanen kauye mene ne manufarku da wannan shiri?
Ai ni ne dai Basafcen, wato ni ne Akta a shirin, amma jagoran wannan shirin shi ne Alhaji Yusuf Ladan dan Iyan Zazzau shi ne yake rubutawa, kuma shi ne mai shiryawa ni kuma ni ne nakan yi Basafcen domin Basafce shi ne babban jarumin shirin, wato akta, shi ne wanda ake gaya wa duk ilimin da ake so jama’a su sani da kuma yadda za a wayar wa jama’a kai, saboda haka a cikin wadanda suke shirya wasan ni ne jarumin shirin kuma ni ne Basafce dan Malam Dogara Na Kumatu Mai Karen Kamun Kura, kuma an kirkiri shirin ne domin a wayar wa mutane kai su san muhimmancin maganin kwari da takin zamani da iri masu kyau domin amfanin gona ya yi kyau.
Aminiya:Kamar maganar talla da kake yi a gidan rediyo shin gidan rediyo ke saka ko kamfani?
Talla a aikin jarida ribar kafa ce, domin a lokacin da nake aikin da BBC na samu wani lokaci na koyi yadda ake karatun talla, to su tallace-tallace da ka ji na yi, kamar na su Kabo da sauransu, wannan abu ne da ni na kirkira da kaina, ni na kirkiro da kaina, amma kuma babu dan Adam da yake cewa shi ya isa. Kuma wata sa’a muna zaune da abokan aiki wani zai fadi wani abu ko wata karin magana sai in dauke ta in juya ta, ko kuma wani ya zo ya ce ya ji kaza, ita ma sai na dauka in yi amfani da ita, to cikin yardar Allah kuma sai ka ga an dace ya fito yadda ake so kuma ya karbu kamar yadda ake so.
Aminiya: Karin maganar da kake yi a ina ka koyo, ko wajen kakani ka koya?
Ina zato zama da tsofaffi da kuma saurare na natsuwa, yawancin sauraren na ilimi yana da amfani idan ka zauna kana sauraro ba ka musu kuma ba ka dakilewa kuma ba ka cewa kaza-da-kaza sai dai, idan an gama kana iya tambayar abin da ba ka gane ba. To muna zama da mutane haka ana magana kuma na karin magana a inda ba ka gane ba, to sai ka yi tambaya, domin ka san ita Hausa albarkar da ke cikinta yawa gare shi duk inda ka dauko wani lokaci sai ka ga ya wuce, kuma a dace.
Aminiya:To, kamar Karin maganar da kake yi wajen talla ko akwai wanda kake shan korafi daga jama’a?
Akwai guda daya da muka yi da wanda ake kira Usman Yaro, Allah Ya gafarta masa, wanda nake kiransa Manu, domin a kan tallar da na tambaye shi cewa yaya zai tafi wuri kaza da wuri kaza? Sai ya ce ai wannan Malam sai zuciya, ni kuma sai na ce su zuciya manya! To a kan wannan sai in ce kira a waya da sako ban samu kamarsu ba da tambayoyi. Sai kuma dayan da nake cewa “Tiki Sa dan agaji ya ga babban soja,” wasu suka kira suna zagi mai zai sa a hada agaji da wannan? Wasu in suka kira su ce mai zai sa in kawo maganan soja da agaji, wasu suna fada, wasu kuma abin ya yi musu dadi da aka gwama dan agaji da soja, domin ga soja da cikakken kaki shi ma dan agaji ga shi da cikkkaken kakinsa, kuma ya ga babban soja ya ce “Tiki Sa!” Shi ke nan.
Aminiya:Ranka ya dade yaya kuke da Manu?
Yadda muke da Manu shi ne abokina ne, kuma daga karshe ya zama dan uwana, domin na auri yayarsa, kuma sunansa Usman Yaro (Allah Ya gafarta masa) su mutanen Raba ne da ke Jihar Sakkwato, kuma duk kusan shirin talla da nake yi tare muke yi da shi.
Aminiya:To, yaya kake ganin aikin jarida a da da na yanzu?
To, komai da zamaninsa, domin shi aikin jarida abu ne rayyaye, kuma komai yana tafiya da zamaninsa ne, wasu suna cewa aikin jarida ya lalace, ni kuma ban yarda aikin jarida ya lalace ba, sai dai kawai mafi yawan ma’aikatan suna son kansu ne ba al’umma ba, kuma ba su taba bada labarai irin na nishadi sai dai kullum labarin tashin hankali. Yau ka ji an kashe wane ko kuma yaki ya balle can. Kamata ya yi su rika shiga kauye suna ganawa da manoma domin jin yadda suka samu amfanin gona ko yadda kiwo yake kansacewa.
Aminiya: Wace shawara za ka ba wadanda suke aikin a yanzu?
To, zan tuna masu abin da suka sani ne na amana da ke kansu, domin yanzu kamar misali jaridarka ta Aminiya wani zai iya ratsewa da wallahi a jaridar Aminiya ya gani domin ya san Aminiya ba za ta buga labarin karya ba, duk labarin da za ta fada sai tana da yakinin cewa haka ya faru, don haka lallai ne mu san cewa duk abin da za mu fada, mu fadi gaskiya domin amana ne a kanmu.
Aminiya:Ranka ya dade iyalai fa?
Ina da mace daya, kuma Allah Ya ba ni ’ya’ya guda takwas kuma duk maza, sai dai Allah Ya karbi uku saura biyar. Kuma a halin yanzu ina noma kuma ina da sarauta, ni ne Galadiman Karau-karau, kuma ina daya daga cikin mambobin hukumomin gidajen rediyo har guda biyu, don haka ya sa da farko na ce ba a ritaya a aikin jarida, har zuwa yau ni dan jarida ne.