✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a kai wa Sarkin Kano hari ba —’Yan sanda

Lamari ne da ya shafi hatsari ba hari ba.

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta musanta rahoton da ke yaduwa na cewar an yi yunkurin kai wa ayarin Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero hari.

Tuni jita-jita ta karade cewar an kai wa ayarin Sarkin Kano hari a kan hanyar Zariya a cikin birnin Kano a ranar Lahadi.

  1. ’Yan bindiga sun sako daliban makarantar Bethel 28 a Kaduna
  2. Rikicin APC: Sabuwar takaddama tana ruruwa a Jihar Zamfara

Sai dai Kakakin ‘yan sandan Jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce hatsari ne ya rutsa da motar karshe daga cikin ayarin sarkin ba hari aka kai masa ba.

Kiyawa ya ce, “Lamari ne da ya shafi hatsari ba hari ba.

“Tawagar Sarkin Kanon ta samu hatsarin ne daga Gadar Lado zuwa Gadar Dangi, inda wata mota kirar Toyota Corolla ta yi karo da motar karshe daga cikin ayarin motocin sarkin.

“Direban motar Toyota Corolla an garzaya da shi asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano don ba shi kulawa,” cewar kakakin.

Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne yayin da Sarkin ke hanyarsa ta komawa Fada bayan ya halarci wani taro a Asibitin Ahmadiyya da ke kan titin Zariya a Kano.

Kokarin jin ta bakin Fadar Sarkin kan lamarin ya ci tura, domin duk kiran da aka yi wa mukaddashin Shugaban Ma’aikatan Fadar, Alhaji Ahmad Ado Bayero bai daga wayarsa ba.

Haka kuma bai bayar da amsar sakon kar-ta-kwana da aka aika masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.