✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a daraja marubuta a kasar nan – Maje El-Hajjij

Maje El-Hajjij Hotoro na daya daga cikin mashahuran marubutan Hausa na zamani. Ya kwana biyu ba a ji duriyarsa a duniyar rubutun littafi ba, domin…

Maje El-Hajjij Hotoro na daya daga cikin mashahuran marubutan Hausa na zamani. Ya kwana biyu ba a ji duriyarsa a duniyar rubutun littafi ba, domin kuwa ya mai da alkalaminsa zuwa harkar fina-finai da aikin jarida. Kwatsam sai ga shi ya dawo ruwa, inda ya fitar da sabon littafinsa mai taken: ‘Soyayya Da Sha’awa.’ Aminiya ta tattauna da marubucin, inda ya zazzage mata buhun tarihinsa da sauran bayanai da suka shafi harkar rubutu da sauransu:

 

Shin wane ne Maje?

Wadansu na kirana Dan Baiwa, wadansu su kira ni Jin-ka-ya-fi-ganin-ka. ALA kuma ya yi mini kirari da: “Alkatibi kuma dan jarida, manazarci dan wasan kwaikwayo, komai-da-ruwanka. Maje ka zama cinye du.”

Koma dai mene ne, ina ganin a wasu wuraren ba na bukatar gabatarwa; ba don kowa ya san ni ba face sai domin babu abin gabatarwar. Ni haifaffen Gidan Rijiya ne a Unguwar Hotoro a Karamar Hukumar Nasarawa a Kanon Dabo. Girman Kano, tashin Kano, karatu a Kano daga matsayin makarantar allo zuwa firamare aka matsa sakandare, sannan aka dire a kwaleji. Marubucin littattafai da fina-finan Hausa, manazarci, mawallafi kuma dan jarida sannan mashawarci a kan harkar sadarwa.

Yaushe ka fara rubutun littafi kuma me ya ja hankalinka ga harkar rubuce-rubuce?

Na fara rubuta littafi tun ina kusan ajin karshe a makarantar firamare. Kuma abin da ya fara jan hankalina shi ne littafin Magana Jari Ce da malaminmu yake karanta mana. Sai kuma nazartar littattafan Hausa, da yake na kasance ma’abocin son karatun littattafan Hausa.

Wane littafi ne ka fara rubutawa kuma wanne ne ya fara shiga kasuwa?

Littafin Shakka Babu na fara rubutawa amma littafin Sirrinsu ne ya fara shiga kasuwa a 1999.

Zuwa yanzu littattafai nawa ka wallafa kuma wanne ne ya fi shiga ranka, ma’ana, wanda ya kasance Bakandamiyarka?

Na wallafa littattafai sun kai 17 kuma Sirrinsu ya fi shiga raina, saboda shi ne littafi irinsa na farko a sansanin marubuta, wanda ya zo da sabon salon da babu irinsa, ya kuma zama silar haskaka alkalamina a duniyar makaranta. Sannan ya zama labari mafi tsada da aka saya aka juya zuwa fim a shekarar 2000 kamar yadda Mujallar Tauraruwa ta wallafa. Wanda har a halin yanzu labarin fim na 1 zuwa 2 Naira 50,000 ake saya. Ba kuma kowa ake saya haka a wajensa ba. Sannan Sirrinsu shi ne sunan I-mal dina kusan shekara goma da budewa. Ina da shafi a dandalin sadarwa da sunan Sirrinsu kuma kamfanina ma a halin yanzu da Sirrinsu Media nake amfani.

Ka fitar da sabon littafi kwanan nan, ko za ka yi bayaninsa a takaice?

Sunan littafin Soyayya Da Sha’awa. Shi wani sabon salon jan hankali ne ga al’umma na halin da masoya da ma’aurata ke kasancewa a sassa daban-daban, musamman a yankunan Hausawa. Soyayya Da Sha’awa, an fara gabatar da shi a zauren sada zumunci na WhatsApp da ake tattauna muhimman batutuwa da suka shafi soyayya ko sha’awa. Wanda daga baya aka rika tattara wasu daga cikin muhimman abubuwan da aka tattauna, kana aka fadada littafin da gudunmawar wasu mambobin zauren da samun bayanai daga kafofin sadarwa na zamani da kuma hange gami da hasashen marubucin. Littafin wani sabon salon rubutu ne da ya hada gamayayyar ra’ayoyin kwararrun marubuta, malamai da manazarta; wanda zai bayar da shawarwari da kuma hannunka mai sanda ga al’ummar Hausawa a kan aure da ma’aurata. Wanda sanin kowa ne, ya isa abin takaici a halin da yau muka tsinci kanmu, yadda aure da yake abu mai matukar muhimmanci da daraja a addinance da kuma al’adance amma yau ya zama tamkar kallabin da za a iya daurawa gami da kwancewa a duk lokacin da aka so. Littafin an kasa shi zuwa kusan kashi hudu. Na farko, domin samari da ’yan mata da ango da amarya da zawarawa da kuma cututtukan mata da kananan yara.

Littafin Kawaliya kuma na fara rubuta shi a Mujallar Fim tun a 2006 amma kasancewar ya yi kamanceceniya da wani sha’anin harkar tsaro da ya jefa kasar nan a cikin wani mummunan yanayi ya sa na dakata saboda wasu dalilai; musamman kasancewar an faro labarin ne daga Maiduguri kuma cikin ikon Allah wani abu ya taso daga can da ya yi kama da na labarin. Shi kuma labari ne na yadda wata gurbatacciyar guba ta kwaranyo daga wasu sassan duniya, wacce kuma take da karfin tasirin sarrafa tunanin mutane ta hanyar mayar da su tamkar wasu dabbobi.

Da ana kukan cewa ka daina fitar da littafi sai labaran fim, me ya sanya yanzu ka dawo da harkar littafi?

Ba daina rubuta littafi na yi ba, na koma rubuta labaran fim ne domin can ma a gwada a gani ko za a iya. Cikin ikon Allah kuma kusan fina-finan da na rubutu sun yi tasiri a wajen masu kallo. Kamar yadda Sirrinsu a matsayinsa na littafina na farko da ya shahara, kazalika shi ma Malika ya zama fim irinsa na farko da ba a taba yin fim mai yawan karin magana kamarsa ba. Domin kamar yadda wani dalibi ya yi nazarin samun digiri a kansa, ya fito da karin magana kusan 300 a ciki. A halin yanzu alhamdu lillahi, na dawo saboda ina da abin rubutawa kana kuma na fahimci kamar masoyana na cike da kishirwar rubutuna.

Wane kalubale ka fuskanta ko kake fuskanta a matsayinka na marubuci?

Na fuskanci wani babban kalubale, lokacin da na yi hasashe a shafina na Sirrinsu da ke jaridar Leadership Hausa, har ta kai wadansu suka yi tattaki takanas daga wata kasa suka gayyace ni domin sanin yaya aka yi na samu wannan masaniya. Duk yadda zan yi na wanke kaina babu wanda ya yarda da ni. Haka suka sa ni a gaba da bibiya, ba dare ba rana domin dauka ta a matsayin Gizon da ya sharara musu karya tare da boye wani muhimmin bayanin sirri.

Yaya kake ganin za a inganta harkar rubutun Hausa a kasar nan, ta yadda marubutan Hausa za su yi alfahari kamar takwarorinsu na duniya?

Hada marubutan Hausa da sauran takwarorinsu na duniya kamar kwatanta mulkin Shugaban Kasa ne da na Kansila. Domin a nan marubucin Hausa yana daraja ne kadai a idon makaranta. Idan ka dauke matar marigayi Bashir Karaye da ta karrama marubuta, ban yi tsammanin akwai wanda ya kara kwatanta wannan kokarin ba. Babu ruwan gwamnatoci da waiwayen marubuci, ba su ma sa shi a sahun wani muhimmin abu. Sannan mutanenmu na da gandar karatu, sun fi son ji da kuma gani amma ba karantawa ba. Kusan kowa ya koma kafafen sadarwa a wayoyin salula. Misali, wata rana wani dalili ya sa na kai ziyara Landan sai abokan tafiya ta suka tambaye ni, me nake so a matsayin tsaraba? Na ce littattafai. Suka kai ni katafaren shagon sayar da littafi fiye da girman wasu manyan shaguna a Jihar Kano. Na shiga na rika kwasar littattafai, ga su nan birjik an killace su. Kowane da farashinsa like a jiki. Mafi karancin farashi shi ne na fam 99, wanda a kudin Najeriya idan ka auna nawa ne? Amma a nan a littafi ya kai Naira 300, ya zama kaya a kasuwa. Sannan a nan waye zai bude makeken shago kawai domin sayar da littattafan Hausa? Don haka bambancin marubutan nan da na duniya kamar bambancin sama da kasa ne.

Me ka samu albarkar rubutu, wanda ba za ka taba mancewa da shi ba a rayuwarka?

Kamar yadda duk abin da daki ya samu albarkacin kofa ce, haka ni ma kusan duk abin da na samu a rayuwa Allah ne sila kuma albarkacin rubutu ne. Na farko, samun satifiket din karramawa a gasar Injiniya Bashir Karaye. A gaban manyan mutane, a gaban manema labarai, a tsakiyar Birnin Tarayya aka karrama ni a matsayina na marubucin Hausa. Wannan abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwata. Na kuma samu sanayyar mutane daban-daban na masoya, kamar yadda na zagaya wasu kasashen duniya da ko a mafarki ban yi tsammanin zuwansu ba.

Yaya kake ganin harkar kungiyoyin marubuta, ko tana da fa’ida kuwa?

Maganar gaskiya ban taba shiga wata kungiyar marubuta ba sai yanzu da nake cikin Kungiyar Marubuta Fina-Finai Zalla (Kaswa). Don haka ban san komai game da harkar kungiya ba. Amma dai ina da labarin suna gudanar da taro lokaci zuwa lokaci, suna bitar rubutu da kuma wakoki.