Shugaban kungiyar Magoya Bayan Nasarawa United da ke Jihar Nasarawa Salisu Galadima da aka fi sani da Atakinbasiya ya karyata labarin da aka baza cewa an dakatar da shi tare da Sakatarensa Abdulsalami Abubakar kan zargin yin sama-da-fadi da kudin kungiyar.
Shugaban ya ce babu kanshin gaskiya a labarin, hasalima har yanzu shi ne shugaba tare da sakatarensa Abdulsalami Abubakar kuma babu gaskiya a labarin da aka yi a kansu cewa sun yi sama-da-fadi da dukiyar kungiyar.
A lokacin da yake tattaunawa da wakilin Aminiya, Shugaba Salisu Galadima ya kalulabanci duk wani mai hujja a kan an dakatar da su da ya gabatar da haka ga duniya kuma shi a iya saninsa a kullum yana samun yabo ne a bisa irin jagorancin da yake yi maimakon kushewa, kamar yadda wasu ke yayatawa.
Daga nan ya ja kunnen wadanda suke baza irin wannan jita-jita da su yi taka-tsan-tsan idan ba haka zai dauki matakin shari’a a kansu. “Wadansu makiya ne ke baza irin wannan jita-jita don bata mini suna kuma idan ba su yi hankali ba zan dauki hukunci a kansu”, inji shi.
Sai ya bukaci magoya bayan kungiyar da sauran membobin kwamitin gudanarwa da su yi watsi da wannan jita-jita kuma ya hore su da su hada kai don ganin kulob din ya ci gaba da samun daukaka a ciki da wajen Najeriya.
Idan za a tuna, a jaridar Aminiya ta makon jiya ce aka bayar da labarin dakatar da shugaban tare da sakatarensa a bisa zargin sun yi almundahana da dukiyar kungiyar.
Ba a dakatar da ni a matsayin shugaban kungiyar Magoya Bayan Nasarawa United ba -Salisu Galadima
Shugaban kungiyar Magoya Bayan Nasarawa United da ke Jihar Nasarawa Salisu Galadima da aka fi sani da Atakinbasiya ya karyata labarin da aka baza cewa…
