✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a ba wa Matan karkara muhimmanci a gwamnati a Najeriya —MDD

Mata suna fuskantar kalubale na rashin jin muryarsu a gwamnatance.

Mataimakin Wakiliyar Mata ta Majalisar Dinkin Duniya, Mista Lansana Wonneh ya ce duk da matan karkara a Najeriya na noma ka’in-da-na’in, ba a ba su muhimmanci ko kadan a gwamnatance.

Wonneh ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Jihar Kalaba, yayin Bikin Ranar Matan Karkara ta Duniya da Majalisar Dinkin Duniyar da hadin gwiwar Kungiyar Mata Kiristoci ta (WOWICAN) suka shirya.

Taken bikin na bana dai shi ne ‘Matan Karkara Na Noma Abinci Mai Kyau Ga Kowa’.

Wonneh ya ce an shirya taron ne domin zaburar da mata mazauna karkarar da ke kokarin samarwa, da sarrafawa, hadi da tattata abinci don ciyar da al’umma, duk da watsi da su da ake yi a kasar.

Ya ce Majalisar Dinkin Duniya za ta hada kai da Gwamnatin Najeriya domin kawo gyara a lamarin.

“Yayin da mata ke aiki tukuru wajen samar da abinci, suna fuskantar kalubale na rashin jin muryarsu a gwamnatance, ko a abubuwan da suka shafe su kai tsaye.

“Muna so mu tabbatar da wadannan mata su san ‘yancinsu, sun kuma samu isassun kayan noma, domin samun karin kudin shiga da kuma kula da ’ya’yansu”, in ji shi.

A nata bangaren, Shugabar WOWICAN ta kasa, Misis Victoria Ihesiulor, ta ce karfafa guiwar matan a harkar noma, babbar hanya ce ta yaki da matsanancin talauci da yunwa da karancin abinci mai gina jiki.