Minista a Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, Umar Ibrahim El-Yakub, ya ce gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta samar da yanayi mai kyau domin bunkasa kasuwanci a Najeriya.
Ya kuma ce gwamnatin ta shimfida ayyukan raya kasa a fadin Najeriya da za su taimaka wa habakar tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi.
- Ku kuka talauta ’yan Najeriya —Gwamnoni ga Gwamnatin Tarayya
- Birrai sun yi dabdala a tsakiyar birni a Thailand
Ministan ya fadi haka ne lokacin da yake jawabi a bikin bude kasuwar bajekoli ta duniya ta jihar Kano (KACCIMA) karo na 43 a Kano ranar Asabar.
A cewar Umar El-Yakub, “Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta samar da yanayi mai kyau da ‘yan kasuwa da kuma kasuwanci ke bukata domin su bunkasa, musamman ta fannin samar da tituna da layukan dogo da za su sada ilahirin sassan Najeriya har ma da makwabtan kasashe.
“Idan aka dauki layin dogon Legas zuwa Ibada zuwa Abuja, da na Abuja zuwa Kaduna, da na Kaduna zuwa Kano, da wanda zai tashi daga Kano ya bi ta Katsina har ya dangana da Maradi a jamhuriyar Nijar, da titunan da ake shimfidawa a sassan kasar daban-daban, ayyuka ne da za su saukaka sufuri sannan ya saukaka fitar da kaya daga Najeriya zuwa ketare.
“Sannan ga aikin jawo iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano (AKK), wanda shi ma da zarar an kammala zai taimaka wajen karfafa sabbin masana’antu, sannan wadanda suka durkushe ma za su farfado. Ga kuma aikin tashar jiragen ruwa ta tsandauri ta Dala wacce ita ma ake dab da budewa a Kano.
“Yana daya daga cikin abubuwan da ke sa ni farin ciki shi ne na je kasashen waje na kayayyakin da aka sarrafa a Najeriya a cikin manyan kantunansu, wannan kuma ya samu ne saboda inganta harkar tattalin arziki da gwamnatinmu ta yi,” inji Umar El-Yakub.
Ministan ya kuma zagaya kasuwar, inda ya ce ya yi farin ciki da kayayyakin da ya ga an bejokolinsu a ciki, inda ya yi alkawarin ci gaba da jajircewar gwamnatinsu wajen biyan bukatun ’yan kasuwa.
Shi ma a nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce sannu a hankali matsayin jihar Kano na cibiyar masana’antu ya fara dawowa inda ya ce yanzu jihar ce ke kan gaba wajen sarrafa shinkafa a Najeriya.
Ganduje, wanda Kwamishinan Kasuwanci na jihar, Barista Ibrahim Mukhtar ya wakilta, ya ce, “Yanzu sama da kaso 50 cikin 100 ma shinkafar da ake sarrafawa a Najeriya, masana’antun Kano ne suke gyara ta.
“Hakan kuma ya faru ne sakamakon samar da yanayin kasuwanci mai kyau da gwamnatin jihar da ta tarayya suka yi, musamman ta fuskar samar da tsaro da ayyukan raya kasa wadanda suke jan hankalin masu zuba jari,” inji shi.
Kasuwar ta bajekoli ta Kano wacce ta aka kafa kusan shekara 100 da suka gabata a bana ta fara ci ne daga ranar 30 ga watan Nuwamba har zuwa 13 ga watan Disamban 2022.