Hukumar Samar da Ayyukan yi ta Kasa (NDE), ta fara horas da wasu mutum 100 kan ayyukan noma karkashin shirinta na Sustainable Agricultural Training scheme (SADTS) a Jihar Kaduna.
Wadanda ake horarwa sun hada da maza da mata daga kananan hukumomin Kaduna, kuma za su kwashe watanni uku suna karbar horon.
- Tsadar abinci na barazanar kawo yunwa a Najeriya —Gambari
- Shigo da masara: Manoma sun fusata da Buhari
Da yake kaddamar da horon, Shugaban Hukumar NDE na jihar, Nasiru Ladan Mohammed Argungun ya bukaci matasan sun mayar da hankali sosai.
Ya kuma ce za su koyar da su abubuwan da suka jibanci harkar noma.
“Wa’adin horarwar watannin uku ne, kuma za su koyi bangarorin noman dabbobi da na tsirrai a karance da kuma zahiri”, inji wanda ya wakilce Shugaban, Sani Maiwada.
Ya kuma ce, sana’ar dogaro da kai ita ce maganin zaman kashe wando, saboda aikn gwamnati ya yi karanci.
Ya gargadi masu karbar horon cewar duk wanda bai samu kashi 75 ba na yawan shiga aji ba, to ba za su ba shi shaidar kammala horon ba.
Ya kuma ce wadanda suka kammala horon kuma za su karbi takadar shaidar kammalawa.