Aiyukan kungiyar Boko Haram sun kara yawan mahaukata da masu fama da lalurar tabin hankali ta hanyar basu miyagun kwayoyi a yankin.
Shugaban Asibitin Masu Tabin Hankali na Maiduguri, Dokta Ibrahim Abdullahi Wakawa ya fada wa Aminiya cewa “Akwai sabbin hanyoyin amfani da miyagun kwayoyi da aka bullo da su”.
Ya bayyana cewa jama’a na amfani da wasu magungunan da ake amfani da su a wasu yankin Arewaci na kasar Kamaru da Kudancin kasar Chad da Nijar saboda barkewar rikici a yankunan.