A ranar 20 ga watan Satumba, 2023 ne, Kotun Shari’ar Zabe ta Jihar Kano ta soke nasarar da Gwamnan Jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP, ya samu tare da bayyana Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar.
Sai dai za a iya cewa maimakon hukuncin kotun ya kashe wa Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida gwiwa, sai ya zame kamar an kara masa karfi inda ya ci gaba da gudanar da ayyuka a jihar.
- Zaɓen Kano: Ranar Litinin Kotun Daukaka Kara Za Ta Saurari Karar Abba
- BUA da Dangote na zargin yi wa juna zagon kasa a harkokin kasuwanci
Idan za a iya tunawa a jawabin Gwamnan a wajen taron manema labarai da ya yi jim kadan bayan yanke hukuncin ya ce, “Wannan hukunci ba zai kashe mana gwiwa wajen ci gaba da yi wa al’umma ayyukan raya kasa ba.
“Tuni muka umarci lauyoyinmu su gagaguta daukaka kara domin dawo da hakkin al’umma. Abu ne da yake a fili mu muka lashe zaben da aka yi a watan Maris da kuri’u mafiya rinjaye, amma bangaren ’yan hamayya suka je kotu suka kalubalanci wannan nasara ta al’ummar Jihar Kano.”
Masu sharhi sun ce ga dukkan alamu Gwamnan da gaske yake kan wannan batu, domin ya ci gaba da gudanar da ayyuka a jihar duk da hukuncin.
Daga cikin ayyukan da ya gudanar akwai amfani da tallafiin rage radadi da Gwamnatin Tarayya ta ba jihar na Naira biliyan biyar wajen sayo kayan abinci inda ta raba kimanin buhu 800 na kayan abinci da suka hada da shinkafa da masara ga kowace mazaba daga mazabu 830 da ke jihar.
Kuma Aminiya ta gano a yanzu haka ana ci gaba da gudanar da rabon kayan abincin a masallatai da gidajen marasa galihu da sauransu.
Haka a kwanakin baya Gwamnan ya gabatar da kwarya-kwaryar kasafin kudi ga Majalisar Dokokin Jihar, kasafin da ya kunshi Naira biliyan 58.
Har ila yau Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rabon kayan koyo da koyarwa ga makarantun firamare da sakandare inda ya rarraba kayan makaranta da littattafai da kudinsu ya kai Naira miliyan 50 ga makarantun da ke kananna hukumomi 44 na jihar.
Baya ga wannan Gwamnan ya gudanar da Auren Gata da aka fi sani da Auren Zawarawa ga mutum 1800 a jihar, inda ya yi amfanin da kudin jihar wajen taimaka wa rayuwar sababbin ma’auratan ta hanyar saya musu kayan daki da garar abinci da kuma wasu kudi da aka ba amaren da nufin jan jari don dogaro da kansu.
Haka a ranar Juma’ar da ta gabata, Gwamnan ya gabatar da cikkaken kasafin kudin 2024 ga Majalisar Dokokin Jihar a karkashin jagorancin Shugabanta Alhaji Jibril Falgore. Tuni majalisar ta amince da kasafin kudin da ya kai Naira biliyan 350.
Har ila yau kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da tura daliban Jihar Kano 1001 don yin karatun digiri na biyu a kasashen waje da dama.
Tuni rukunin farko da na biyu da suka kunshi dalibai 206 suka tafi kasashen da za su yi karatu da suka hada da Indiya da Uganda da sauransu.
Haka Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fara gudanar da aikin gyaran gadar sama ta Kofar Nasarawa.
A lokacin da yake bayani game da sake gyaran gadar Gwamnan ya ce ya zama dole gwamnatinsa ta gudanar da wannan aiki lura da yanayin da gadar take ciki wanda ka iya jawo matsala ga masu amfani da ita.
Har ila yau Gwamna Abba K. Yuusf ya ci gaba da gudanar da aikin tituna na kilomita biyar-biyar a dukkan kananan hukumomin jihar 44.
Tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya bayar da aikin a shekarar 2015 don yin kilomita biyar-biyar da za a iya cewa Gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje da ta yi shekara 8 ba kammala ba.
Hakan ya sa gwamnatin ta Abba ta waiwayi aikin tare da bayar da umarni ga ’yan kwangilar su dawo bakin aiki don kammalawa ba tare da bata lokaci ba.
Haka kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauki nauyin wata yarinya mai suna Nana Muhammad don yi mata maganin ciwon ido a kasar Indiya.
Kuma a makon jiya an ga Gwamnan a wani asibiti wajen wata yarinya mai fama da ciwo a kafa, inda ya biya mata kudin aiki, sannan ya ba iyayenta kudin da za su rike a hannu, sannan kuma ya bi kowane gado yana ba majinyata Naira dubu 50.
Zuwa asibitin ya yi matukar jan hankalin mutane, ciki har da ’yan adawa, inda da yawansu suke bayyana shi da mutum mai tausayi da son talakawa da kananan yara.
Haka kuma ya gyara Asibitin Yara na Asiya Bayero, wanda tuni ya dawo aiki sosai, inda ake bayar da magani kyauta.
A yanzu haka Gwamnatin Abba K. Yusuf ta ware kimanin Naira biliyan shida don biyan ’yan fansho 500 a jihar wadanda gwamnatin ta ce sun dauki tsawon lokaci suna bin kudinsu a hannun tsohuwar gwamnatin amma ba su samu ba.