Hukumar Kwallon Kafar Najeriya NFF ta sanar da cewa Augustin Eguavoen ne zai ci gaba da kasancewa mai horas da yan wasan tawagar Super Eagles na wucin gadi.
NFF ta ce mai horas da kungiyar na riko Augustine Eguavoen zai ci gaba da aikin da yake kai.
- Tsagin Shekarau ya yi fatali da sulhun uwar jam’iyya kan rikicin APC a Kano
- Cutar tamowa na barazana ga mutum miliyan 13 a Gabashin Afirka
Wannan dai na zuwa ne yayin da Hukumar NFF ta sauya fasalin tawagar masu horar da ’yan wasan kasar a ranar Litinin biyo bayan watsin da ta yi da batun dauko wani sabon koci daga ketare.
Sanarwar ta kuma fito karara ta bayyana cewa ta dakatar da yarjejeniyar da ta tsara kullawa da Jose Peseiro, wanda aka sa ran cewa zai karbi aiki daga Eguavoen da zarar an kammala gasar cin kofin nahiyar Afirka.
Sanarwar wadda ta samu sa hannun daraktan yada labaran Hukumar NFF, Ademola Olajire ta ce tsohon shahararren dan wasan kasar, kuma tsohon kocin tawagar kwallon kafar kasar ta ’yan kasa da shekaru 20, Emmanuel Amuneke ya zama mataimakinsa.
Amuneke na daya daga cikin zaratan ’yan wasan Najeriya da suka lashe kofin Afirka a shekarar 1994, kuma shi ne ya ci kwallaye biyun da suka bai wa kasar nasara a wasan karshe da ta fafata da Zambia a birnin Tunis na Tunisia.
Ya kuma ci kwallaye biyu da ta bai wa Najeriya nasarar lashe gasar kwallon kafa a Olympics a karo na farko a shekarar 1996, ya kuma ci kwallaye 2 a gasar cin kofin kwallon kafa a 1994 a Amurka.
A matsayinsa na mai horarwa, ya kai tawagar kwallon kafar Tanzania kofin gasar kofin Afrika a 2019 a Masar.
Sauran wadanda sauye sauyen na Hukumar NFF ya shafa sun hada Salisu Yusuf a matsayin mataimakin koci na biyu, Joseph Yobo – matamakin koci na uku, sai kuma Aloysius Agu – mai horas da masu tsaron raga.