Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta bukaci a gaggauta binciken fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Gadon Ƙaya, kan zargin da ya yi na auren jinsi a jihar.
Majalisar ta bukaci haka ne bayan takardar gayyata da Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi ta aike wa fitaccen malamin mazaunin Jihar Kano.
Majalisar dokokin jihar Bauchi tana neman hukumar ta binciki zan da malamin ya yi kan batun taron auren jinsi da ya ce an yi a jihar, wanda hakan ya saɓa wa koyarwar Musulunci da Kiristanci.
Hakan dai ya biyo bayan wani bidiyon Sheikh Abdullah Gadon Ƙaya, da ya tayar da ƙura a kafofin sada zumunta.
- Kwastam ta kama kayan sojoji da ƙwayar N31bn
- Ƙarin Kuɗin Fetur: Hauhawar farashin kaya na iya ƙaruwa —MAN
A cikin bidiyon, an ji malamin yana cewa wani ya ba shaida masa cewa ’yan luwaɗi da maɗigo daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya sun gudanar da taro a Jihar Bauchin.
Ya kara da cewa mahalartan sun kuma yi auren jinsi a lokacin taron nasu.
Sai dai bai bayyana wurin da aka yi taron ko lokacin da aka gudanar da shi ba.
Ɗan majalisar jihar mai wakiltar mazaɓar Chinade/Madara, Nasiru Ahmed Ala, ya gabatar da ƙudurin neman a gayyato malamin bisa buƙatar gaggawa lura da muhimmanci lamarin.
Dakta Nasiru Ahmed Ala, ya ce Sheikh Gadon-Kaya, ya jaddada muhimmancin hukumar Shari’a ta gayyaci malamin ya yi ƙarin haske tabbatar da doka ta yi aiki a kan duk wanda aka samu da laifi.
Shugaban majalisar, Abubakar Y. Sulaiman, ya ce, kundin tsarin mulkin ƙasa ya ba ta ikon gayyatar kai tsaye ga wani mutum da ya bayyana a gabanta domin gudanar da wani bincike ko neman ƙarin haske kan kowane lamari ko iƙirarin da ya yi.