Fitaccen malamin addinin Musulunci nan na jihar, Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce ya yi waya da Ummakulsum Buhari wato Ummita, kan halin da take ciki sati guda kafin kashe ta.
Malamin ya ce marigayiyar ta kira shi ne a waya don neman shawararsa kan kin amincewa ta auri dan Chinan da magabatanta suka yi.
- NAJERIYA A YAU: Yanka 11 Na Gani A Jikin Ummita —Mai Wankan Gawa
- Kafar Daily Trust ta bude shagon sayayya na intanet
Daurawa ya ce a lokacin ya nuna mata magabatan nata sun fi ta gaskiya, domin rashin sanin asalin masoyin nata mai suna Gheng Quanrong kafin aure, na da hatsari.
Ya ce don haka ya sanya mata wasu sharuda biyar da ya ce idan ta cika su, da kansa zai shige gaba wajen jan hankalin magabatan nata su amince da auren.
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa sharuddan da Daurawan ya shimfida mata sun hada da tuntubar Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) domin tabbatar da sahihancin shigowarsa Najeriya da aikin da yake yi, da kuma nasabarsa.
Kazalika, Daurawa ya ce kasancewar Sarkin Kano ya nada Shugaban China a jihar, zai saukaka mata binciken a kansa.
Sai kuma sanar da Hukumar kula da shige da ficen cewa dan Chinan na shirin auren’yar Najeriya, don jin martaninsu kan lamarin.
Sai kuma Sharadin karshe da ya kafa mata, na sanar da Hukumar Hisba ta jihar Kano domin su koyar da shi Musulinci sosai, kasancewar ance ya musulunta.
Sai dai Daurawa ya ce Ummitan ta dage kan iyayensa sun amince ya aure ta, magabatanta ne suka ki yarda.
A karshe malamin ya ce ta amince da aiwatar da shawarwarin da ya bata, bayan ya tabbatar mata cewa da zarar ta kammala su ba tare da wata matsala ba, zai ja hankalin magabatan nata su amince da auren nasu.
Sheikh Daurawa ya ci gaba da cewa, addinin Musulinci bai haramta wa Musulmi auren wani jinsin mutane ba, matukar sun cika ka’idar aure ta addinin.