✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aure maganin mugun aiki a cikin al’umma

Na ambaci wannan kalma ce ba don cin zarafi ko cin mutumcin kowa ba, sai domin dan abin da zan iya ba da tawa gudummawar…

Na ambaci wannan kalma ce ba don cin zarafi ko cin mutumcin kowa ba, sai domin dan abin da zan iya ba da tawa gudummawar a kan wannan al’amari mai matukar muhimanci wanda kuma shi ne tubalin gina al’umma a jiya da yau da gobe. Muhimmancin aure sai dai malamai su yi abin da za su iya yi a bangaren bayanai. Da fatan masu aure da suka dade a ciki Allah Ya ba su ikon yin hakuri da juna da juriya wurin yin dawainiyar yau da kullum. Wadanda kuma ba su da auren su ma fatammu su dace da mata na kwarai, hakan ne zai samar da al’umma managarciya mai amfani.

Kafar labarai ta BBC Hausa a shekarun baya ta yi wani shiri na Ra’ayi Riga inda aka yi magana a kan aure, kuma muka tattauna a kan yadda Gwamnatin Kano ta wancan lokacin a karkashin Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso da Hukumar Hizbah suka dasa harsashin gina auratayya wacce har zuwa yau ana ci gaba. An tattauna da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kwamandan Hukumar Hizbah  da Mataimakin Gwamna a wancan lokacin wanda yau shi ne Gwamna wato Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, da kuma Hajiya Altine Abdullahi, Shugabar kungiyar Zawarawa ta Jihar Kano, sai kuma ni Mukhtar. 

Don haka ne a yau nake amfani da wannan dama in sake yin tsokaci a kan lamarin aure. A karon farko a masarautar dambatta, Hakimin garin da dattawan gari suka so su takaita matsalar tsadar aure ta inda suka samu mabambantan ra’ayi: wasu na yabo wasu na suka. 

Duka dai ina so mu fahimci wani abu guda ne: aure ibada ne, kuma kada mu manta a kwanakin baya ne aka sanar da mutuwar wani mutum mai suna Malam Bello Masaba mai mata sama da 100  da ’ya’ya sama da 200, amma har ya gama rayuwarsa ba a iya raba shi da matan ba, ashe yadda Gwamnatin Kano da Hukumar Hizbah suke kokarin lalubo masu bukatar aure kuma wadanda da dama ba su da wadata su aurar da su sai sambarka, maimakon munanan kalamai a gare su kuma lallai aure ba ya kawo talauci.

Misali na taba yin aure kuma na ga wadanda sun zarta shekaruna ba aure kuma a cikin rashin wadata, haka na ga wadanda ke da mata biyu  da mai uku, da mai hudu amma gwauro ya je ya amshi abinci daga gare su, to ina maganar cewa aure na hana yin kudi, ko yana kawo talauci? 

Kuma wani lamari mai muhimmanci ga ma’aurata shi ne natsuwa da kamun kai, domin da dama aikata fyade ko masu luwadi da mata masu neman mata ’yan uwansu duka mafi yawa ba su da aure ne.

Nakan jinjina wa Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II a kan kallon illar masu aure ba abin yi ko kuma masu aure su tozarta matan. 

Ya kamata malamai su kara himmatuwa wajen ilimantar da mutane ainihin wane ne ya kamata a ba aure kuma wane ne ke ba da auren, domin da dama idan mai dukiya ya zo ba a duba cancanta kuma da dama ba ai masa surutu idan wani lamari ya bijiro na rashin kyautawa ga auren, sai talaka wanda ke nema da kyar shi ake sa wa ido ko kuma a yi masa surutu. Wannan lamarin shi ma sai malamai sun kara magana. 

Daga karshe ina rokon Allah Ya zaunar da dukan ma’aurata lafiya kuma Ya ba da zuriya mai amfani wacce za ta amfanar a yau da gobe.

Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina. 07066434519, 08080140820